Gwamnoni Sun Taso da Batun 'Karfin Iko' yayin da Ake Shirin Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

Gwamnoni Sun Taso da Batun 'Karfin Iko' yayin da Ake Shirin Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

  • Gwamnoni sun fara neman a kara masu karfin iko a harkokin tsaro yayin da ake kokarin kafa rundunar yan sandan jihohi a Najeriya
  • Hakan na kunshe a cikin rahoton bayan taro da Antoni Janar na jihohi suka gudanar a sakatariyar kungiyar gwamnoni da ke Abuja
  • Rahoton ya nuna cewa mahalarta taron sun yi nazari kan wasu tanade-tanaden da ke gaban Majalisar Tarayya musamnan kan ikon gwamnoni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnonin Najeriya sun nemi a ba su karin karfin iko a kundin tsarin mulki kan harkokin tsaro a jihohinsu tare da samar da tsarin kudaden gudanar da rundunar ‘yan sandan jihohi da ake shirin kafawa.

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton wani taro da Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta shirya a Abuja tare da Antoni Janar na jihohi, masana harkokin shari’a da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fadi wasu matakai da suka dauka da aka fara zaben gwamnan Ekiti

Gwamnoni.
Gwamnonin jihohi na gudanar da taro a sakatariyar kungiyarsu ta NGF da ke Abuja Hoto: @NGFSecretariat
Source: Twitter

Ana son sabunta tsarin tsaron kasa

Punch ta ce rahoton ya bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan daidaita shawarwari domin samar da tsarin doka da na kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohi damar kafa rundunar ‘yan sandansu.

A cewar rahoton, wannan wani muhimmin mataki ne na inganta tsarin tsaron Najeriya ta hanyar samar da tsarin ‘yan sanda da ya fi kusanci da al’umma tare da kiyaye hadin kan kasa.

Gwamnoni na neman karin iko

Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka fito daga taron shi ne bukatar a kara fayyace rawar da gwamnoni za su taka wajen jagorantar ayyukan tsaro a jihohinsu.

Rahoton ya nuna cewa mahalarta taron sun yi nazari kan wasu tanade-tanaden da ke gaban Majalisar Tarayya, musamman wadanda suka shafi karfin ikon gwamnoni wajen ba da umarni kan ayyukan tsaro.

“An jaddada muhimmancin amincewa da rawar da gwamnoni ke takawa wajen daidaita harkokin tsaro a jihohinsu tare da samar da kariya ga kwarewa, gaskiya da ‘yancin gudanar da aiki,” in ji rahoton.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnoni 36 suka bukaci a yi kafin kafa rundunar yan sandan jihohi a Najeriya

Batun ikon gwamnoni ya sake tasowa

Wannan shawara na iya sake tayar da muhawara kan batun ikon gwamnonin jihohin Najeriya 36 a harkokin tsaro, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Ko da yake ana kallon gwamnoni a matsayin manyan jami’an tsaro na jihohinsu, ba su da cikakken iko kan rundunar ‘yan sanda saboda tana karkashin gwamnatin tarayya.

Yunkurin ya zo ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro da suka hada da ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami, rikice-rikicen kabilanci da sauran munanan laifuka.

Gwamnan Kwara.
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRzaq Hoto: @AARahman
Source: Twitter

Rahoton ya nuna cewa ana ganin kafa ‘yan sandan jihohi a matsayin daya daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance wadannan matsaloli da suka yi wa tsarin ‘yan sanda na kasa nauyi.

Gwamnoni sun jaddada matsayarsu

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jihohi 36 sun sake bayyana cikakken goyon bayansu ga kafa ’yan sandan jihohi domin yakar matsalar tsaro.

Gwamnonin sun bukaci a tabbatar da cewa rundunar yan sandan jihohin da za a kafa ta yi daidai da kundin tsarin mulki, tsarin tarayya da kuma kare hakkokin ’yan kasa.

Matsayar ta fito ne bayan kammala taronsu da suka gudanar a Abuja, wanda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi matsalar tsaro da tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262