Kotu Ta Karbi Shaida a Shari'ar da Ake Zargin El Rufai Ya Yi Kutse a Wayar Nuhu Ribadu
- Hukumar DSS ta fara gabatar da shaida a shari'ar da ake zargin Malam Nasir El-Rufai ya yi wa Nuhu Ribadu kutse a wayar salula
- Lauya Deji Adeyanju ya shaida wa kotu cewa Nasir El-Rufai ya taba cewa sun saurari tattaunawar mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
- A karkashin tambayoyin lauyoyin kariya, Adeyanju ya ce bai ji tsohon gwamnan ya furta cewa shi ne ya yi kutse a wayar NSA ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya bada shaida a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a shari'ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Adeyanju ya shaida wa alkali cewa El-Rufai ya furta a wata hira ta talabijin cewa sun saurari tattaunawar wayar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce Adeyanju shi ne shaida na biyu na masu gabatar da kara a shari’ar da ake yi wa El-Rufai kan zargin kutsen wayar Nuhu Ribadu da kuma karya tsaron kasa.
Abin da Deji Adeyanju ya fada wa kotu
Yayin da lauyan masu gabatar da kara, Oluwole Aladedoye, ke yi masa tambayoyi, Adeyanju ya tabbatar da cewa ya san El-Rufai a matsayin tsohon gwamnan Kaduna.
Masu gabatar da kara sun gabatar da takardar sammaci da aka yi amfani da ita wajen gayyatar Adeyanju zuwa kotu, wadda aka amince da ita a matsayin hujja.
Bayan haka, kotun tarayya ta kalli bidiyon hirar da El-Rufai ya yi, inda Adeyanju ya tabbatar da sahihancinta da kuma kalaman da ake zargin tsohon gwamnan ya yi.
Ya ba DSS bayanin abin da ya gani
Adeyanju ya shaida wa kotu cewa daga baya DSS ta gayyace shi domin ya bayyana abin da ya faru a dakin hirar talabijin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026
A cewarsa, ya tabbatar wa jami’an DSS cewa yana wurin lokacin da El-Rufai ya yi kalaman a kai tsaye.
Ya kara da cewa lokacin da aka kara tambayar El-Rufai a hirar, ya bayyana cewa wani ne ya gudanar da aikin sauraron wayar sannan ya mika bayanan gare shi.
A karkashin tambayoyin da lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, ya yi masa, Adeyanju ya ce bai ji El-Rufai yana cewa shi ne ya yi kutse a layukan wayar Nuhu Ribadu ba.

Source: Getty Images
Kotu ta dage sauraron karar
A yayin zaman, masu gabatar da kara sun kuma gabatar da wata takardar jarida ba tare da adawa daga bangaren lauyoyin El-Fufai ba.
Kotun ta amince da takardar a matsayin hujja kafin daga bisani ta dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga Yuni, 2026 domin ci gaba da shari’ar.
Wane hali El-Rufai ke ciki?
A wani labarin, kun ji cewa hadimin Nasir El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya zargi hukumar ICPC da hana tsohon gwamnan samun kulawar likita duk ciwon ido da yake fama da shi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce Nasir El-Rufai ya koka cewa idanunsa sun kumbura, sun yi ja kuma suna masa kaikayi.
A cewar Adekeye, ‘yan uwa da suka kai wa tsohon gwamnan ziyara sun lura da halin da yake ciki kuma sun roƙi jami’an ICPC su taimaka wajen samar masa da kulawar likita.
Asali: Legit.ng
