Sojoji Sun Ceto Mutane Sama da 40 da 'Yan Ta'addan ISWAP Suka Sace a Borno
- Dakarun sojojin Najeriya sun matsawa 'yan ta'addan Boko Haram da kai hare-hare ta sama da kasa a maboyarsu da ke Borno
- Matsin lambar da aka yi wa 'yan ta'addan ya sanya an samu nasarar ceto mutanen da suke tsare a hannunsu a cikin daji
- Rundunar sojoji ta bayyana cewa za ta ci gaba da matsa lamba ga 'yan ta'adda har sai an tabbatar da fatattakarsu daga yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun rundunar "Operation Hadin Kai" sun ceto mutane 47, wadanda yawancinsu mata ne da yara, daga hannun mambobin kungiyar ISWAP a jihar Borno.
Sojojin sun ceto mutanen ne a gundumar Kangarwa da ke Karamar hukumar Kukawa a jihar Borno a wani aikin ceto da aka gudanar a ranar 20 ga watan Yunin 2026.

Source: Twitter
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da kakakin riko na bangaren yada labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan
Sojoji sun dira maboyar 'yan ta'adda a Katsina, an kashe tantirai da kwato manyan makamai
Dakarun sojoji sun ceto mutane a Borno
Goni ya ce wadanda abun ya shafa sun samu yancinsu ne biyo bayan ci gaba da kai hare-haren sojoji kan maboyar 'yan ta'adda a yankin Tafkin Chadi.
“Rundunar Hadin Gwiwa (Arewa maso Gabas), Operation Hadin Kai (OPHK), ta sake samun wata gagarumar nasara tare da ceto mutane sama da 47, wadanda yawancinsu mata ne da yara wadanda 'yan ta'addan ISWAP suka tsare a Kangarwa, karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno a ranar 20 ga Yuni, 2026."
- Kyaftin Mohammed Goni
Sojoji sun kai hare-hare kan 'yan ISWAP
Ya bayyana cewa an samu nasarar gudanar da aikin ne sakamakon tsananta hare-haren kasa da na sama a kan sansanonin 'yan ta'addan, lamarin da ya tilasta wa 'yan tawayen barin maboyarsu.
“An samu nasarar ceton ne ta hanyar matsin lamba da kuma ci gaba da kai hare-hare da dakarun OPHK suka gudanar a kan maboyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi."
“Hare-haren kasa da na sama sun tilasta wa 'yan ta'addan tserewa daga maboyarsu cikin rudani, wanda hakan ya bai wa mutanen da aka sace damar tserewa daga tsawon lokacin da suka yi a tsare."
- Kyaftin Mohammed Goni
Ana kula da mutanen da aka ceto
A cewar hukumar soji, a halin yanzu mutanen da aka ceto suna samun kulawar likitoci da sauran nau'ukan tallafi a wani amintaccen wuri.
“A halin yanzu kwararrun likitoci suna duba mutanen da aka ceto a wani amintaccen wuri. Ana bayar da tallafin jinkai da ya dace tare da hadin gwiwar hukumomin da abun ya shafa domin saukake komawarsu cikin al'umma daga baya."
- Kyaftin Mohammed Goni

Source: Twitter
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar halalka 'yan ta'adda bayan sun kai hari a maboyarsu da ke Katsina.
Sojojin na rundunar Brigade 17 da ke gudanar da aikin "Operation Clean Sweep III" sun kashe mutane biyu da ake zargi 'yan ta'adda ne a jihar Katsina.
Rundunar sojojin ta ƙwato manyan makamai da sauran kayayyaki a lokacin wani farmakin ba-zata ne da aka kai a maboyar 'yan ta'adda da ke karamar hukumar Matazu.
Asali: Legit.ng
