'Yan Sanda Sun Dauki Mataki kan Mutum 24 da Ake Zargi da Kisan Matar Marabar Jos
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 24 da ake zargi da hannu a kashe wa da kona gawar wata mata a Maraban Jos
- Kotun majistare ta bada umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali har zuwa watan gobe, don ci gaba da sauraron shari’ar
- ‘Yan sanda sun ce sama da mutum 100 na ci gaba da fuskantar bincike kan zargin hannu a wannan mummunan danyen aiki a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 24 a gaban kotun majistare da ke NDA Junction, Kaduna, bisa zargin hannu a kisan wata mata da wasu fusatattun jama’a suka yi a yankin Marabar Jos.
An tuhumi wadanda ake zargin da laiffukan hada baki wajen aikata laifi, tayar da zaune tsaye, barna, lalata kadarorin gwamnati da na ‘yan sanda, da kuma kisan kai.

Source: Twitter
An gurfanar da mutum 24 a Kaduna
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, a cewar rahoton Punch.
Mansir Hassan ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan binciken harin ranar 21 ga watan Yuni da ya yi sanadin mutuwar matar.
A cewar sanarwar, kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2026, tare da bayar da umarnin a tsare dukkan wadanda ake zargin a gidan gyaran hali har zuwa lokacin yanke hukunci.
Hassan ya ce:
“Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 24 a gaban kotun majistare da ke NDA Junction, Kaduna, dangane da mummunan kisan wata mata da jama’a suka yi a Maraban Jos.”
Ana binciken sama da mutum 100
Ya bayyana cewa rundunar ta fara cikakken bincike bayan faruwar lamarin, wanda ya kai ga kama wadanda ake zargin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Rundunar ta kuma bayyana cewa jami'anta suna ci gaba da gudanar da bincike kan sama da mutum 100 kan zargin hannu a harin. Ta za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Source: Original
Gargadi kan daukar doka a hannu
Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta yi Allah wadai da dabi’ar daukar doka a hannu, inda ta yi gargadi ga jama’a da su guji hukunta mutane ba tare da bin doka ba.
Hassan ya ce za a kama duk wanda ya dauki doka a hannunsa a gurfanar da shi bisa tanadin doka, a cewar rahoton Tribune.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Rabiu, ya tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da adalci tare da ci gaba da kare doka da oda a fadin jihar.
An fille kan wata mata a Kaduna
A wani labari, mun ruwaito cewa, mazauna Bwari a Abuja sun gano gawar wata mata mai matsakaicin shekaru ba tare da kai ba a wani gini da ba a kammala ba.
Rahotanni sun nuna cewa warin da ke fita daga ginin ne ya sa mutane suka shiga ciki suka gano gawar matar da aka fille wa kai.
Rundunar ‘yan sanda ta kwashe gawar zuwa asibiti tare da fara bincike domin gano ko wacece da yadda aka kashe ta.
Asali: Legit.ng

