Amnesty Ta Shiga Lamarin Kisan Malamar Islamiyya a Kaduna

Amnesty Ta Shiga Lamarin Kisan Malamar Islamiyya a Kaduna

  • Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta nuna takaicinta kan kisan da aka yi wa wata malamar Islamiyya a Kaduna
  • Amnesty International ta bukaci a gudanar da sahihin bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru kan kisan malamar
  • Kungiyar ta nuna damuwa kuma kan yadda ake kara samun karuwar yawaitar kisan mutane ta hanyar daukar doka a hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta yi kiran da a gudanar da sahihin bincike kan kisan gillar da aka yi wa wata malamar Islamiyya a Kaduna.

Wasu gungun mutane ne dai suka kashe matar mai yara biyar jihar Kaduna ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.

Amnesty ta damu kan kisan malamar Islamiyya a Kaduna
Marigayi Ummulkhairi da aka yi wa kisan gilla a Kaduna Hoto: Hassan Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa Amnesty ta yi Allah wadai da kisan malamar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 21 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

An kashe malamar Islamiyya a Kaduna

Malamar, wadda aka gano sunanta Ummulkhairi, an yi mata kisan gilla ne a yankin Mararaban Jos, wani da ke kan babban titin Kaduna zuwa Zaria, bayan da aka yi mata zargin ƙarya na ƙoƙarin sace yara.

Bisa ga bayanai, Malama Ummulkhairi ta tsaya ne domin tambayar wasu yara hanyar da za ta kai ta gurin taron addini, inda aka ruwaito cewa wasu mata suka zarge ta da yunƙurin sace yaran.

Me Amnesty ta ce kan kisan malamar Islamiyya?

Kungiyar Amnesty International ta yi tir da wannan kisa kuma ta bukaci a gudanar da bincike na tsanaki.

“Amnesty International tana yin tir da mummunan kisan gillan da wasu gungun mutane suka yi wa Malama Ummulkhairi, mahaifiyar yara biyar, a garin Mararaban Jos da ke kan babban titin Kaduna zuwa Zaria a ranar 21 ga watan Yuni, 2026." Inji sanarwar

Ƙungiyar kare haƙƙin ta kuma buƙaci rundunar 'yan sanda da ta binciki zargin cewa jami'an 'yan sanda ne da kansu suka miƙa matar ga gungun mutanen, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka da Peter Obi ya nemi Tinubu ya yi murabus

An zargi 'yan sanda da mika ta ga mutane

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Shaidun gani da ido sun shaida wa Amnesty International cewa yayin da gungun jama'a suka far wa ofishin 'yan sandan, jami'an da ke bakin aiki sun fito da matar fili sannan suka miƙa ta gare su inda suka kashe ta tare da ƙona gawarta."
“Idan har hakan ta tabbata, to wannan nuni ne a fili na gaza sauke nauyi daga ɓangaren jami'an tsaro.”

Amnesty ta koka kan kisan malamar Islamiyya

Amnesty International ta bayyana faruwar lamarin a matsayin wani ɓangare na ƙaruwar al'adar ɗaukar doka a hannu ta hanyar gungun mutane su yi kisa a faɗin Najeriya.

“Abin takaici ne yadda kisan gilla na gungun jama'a ke neman zama ruwan dare a faɗin ƙasa. Mafi yawan lokuta ana yin hakan ne kawai bisa zargi, jita-jita, ko rade-rade.” Inji sanarwar

Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomi da su gano tare da hukunta waɗanda ke da alhakin kisan, sannan su tabbatar da an hukunta duk wani jami'in gwamnati da aka samu da gazawa a cikin ayyukansa.

Kara karanta wannan

Ahmed Makarfi: Tsohon gwamnan Kaduna ya samo mafita ga Tinubu kan rashin tsaro

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ba ta riga ta mayar da martani ba game da zargin da Amnesty International.

An kashe malamar Islamiyya a Kaduna
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yadda aka kashe m​​alamar Islamiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa iyalan malamar Islamiyyar da aka kashe a jihar Kaduna sun bayyana yadda ta rasa ranta.

Mijin malamar Islamiyyar, Aliyu Mohammed, ya ce mutuwar matarsa ta jefa shi cikin ruɗani da baƙin ciki.

Wata yar'uwar matar ta bayyana cewa sai da ta gargadi jami'in 'yan sandan da ya fitar da matar waje kan cewa za a iya kashe ta idan ya yi hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng