An Ware Yanki 1 a Najeriya da ba za a Kafa 'Yan Sandan Jihohi ba
- Majalisar Dattawa ta ce an ware Babban Birnin Tarayya Abuja daga shirin kafa 'yan sandan jihohi ne saboda ba shi da gwamna ko Majalisar Dokokin Jiha
- Sanata Yemi Adaramodu ya ce Abuja na ƙarƙashin gwamnatin tarayya kai tsaye, inda minista ke jagorantar harkokinta a ƙarƙashin Majalisar Zartarwa ta Tarayya
- Bayani ya zo ne yayin da gwamnatin tarayya ke shirin sake fasalin tsarin aikin 'yan sanda da kuma kafa tsarin 'yan sandan jihohi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa aka ware Babban Birnin Tarayya (FCT) daga tsarin kafa 'yan sandan jihohi da ake shirin aiwatarwa a Najeriya.
Majalisar ta ce ba za a haɗa Abuja cikin tsarin ba saboda FCT ba ta da gwamna ko Majalisar Dokokin Jiha, kuma gwamnatin tarayya ce ke kula da harkokin yankin kai tsaye.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa FCT ba ta cikin tsarin da aka tanada na kafa 'yan sandan jihohi.
Babu 'yan sandan jiha a Abuja
Adaramodu ya ce tsarin gudanar da FCT ya bambanta da na sauran jihohi 36 na Najeriya, domin minista ne ke jagorantar yankin a ƙarƙashin Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
PM News ta rahoto ya ƙara da cewa FCT ba ta da majalisar dokokin kanta, domin Majalisar Dokokin Tarayya ce ke yin dokoki da suka shafi Babban Birnin Tarayya.
A cewarsa, wannan ne ya sa 'yan sandan tarayya za su ci gaba da kasancewa masu kula da harkokin tsaro a FCT, maimakon kafa rundunar 'yan sandan FCT mai zaman kanta kamar yadda ake shirin yi a jihohi.

Source: Getty Images
Shirin kafa 'yan sandan jihohi
Wannan bayani ya zo ne yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ƙoƙarin kafa sabon tsarin aikin 'yan sanda sakamakon kiran da ake yi na rarraba ikon 'yan sanda da kuma ba jihohi damar kafa nasu rundunonin.
Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa ana sa ran Tinubu zai karɓi daftarin Dokar Kasa ta Gudanar da Aikin 'Yan Sanda a ranar 3 ga Satumba domin ci gaba da sake fasalin tsarin tsaron ƙasar.
Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa kuma shugaban ƙungiyar da ke aiki kan dokar, Femi Gbajabiamila, ya ce an kuma samar da wata kafar yanar gizo da 'yan Najeriya za su iya aika ra'ayoyi da shawarwari kan dokar.
Nazari kafi kafa 'yan sandan jihohi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa kwamitin da ya tsara tsarin kafa 'yan sandan jihohi ya yi nazari kan tsarin aikin 'yan sanda a ƙasashen Indiya, Amurka da Pakistan.
Disu ya bayyana hakan ne yayin wani taron bita kan 'yan sandan jihohi da aka gudanar a Abuja, inda ya ce kwamitin ya yi cikakken kwatancen tsarin tsaron ƙasashen da ke amfani da 'yan sandan jihohi.
Ya ce an gudanar da binciken ne domin a samar da tsarin da zai dace da Najeriya tare da fahimtar ƙalubalen da ka iya tasowa yayin aiwatar da shi.
Asali: Legit.ng

