Wani Bam da Aka Dasa a cikin Mota Ya Tashi a Wurin Hada Hadar Kasuwanci a Jihar Legas

Wani Bam da Aka Dasa a cikin Mota Ya Tashi a Wurin Hada Hadar Kasuwanci a Jihar Legas

  • Kwamishinan ‘yan sandan Legas ya tabbatar da cewa kasuwar kayayyakin takalma da ke Mushin na cikin aminci bayan fashewar wani bam
  • Rahotin binciken farko ya nuna cewa an dasa bam ɗin ƙarƙashin wata mota a kusa da kasuwa, kuma ya fashe ne lokacin da aka kunna ta
  • Bayanai sun nuna cewa mutum guda ya samu rauni, yayin da jami’an tsaro suka ce ba a gano wani ƙarin bam a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Kwamishinan ‘Yan Sandan Legas, Fatai Tijani, ya tabbatar da fashewar bam a wani yankin da ake harkokin kasuwanci a jihar, amma jami'an tsaro sun shawo kan lamarin a yanzu.

Tijani ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a wurin da lamarin ya faru a Kasuwar Kayayyakin Takalma da ke Mushin, bayan jami’an tsaro sun gudanar da cikakken bincike.

Kara karanta wannan

Turji ya fitar da sabon bidiyo, ya bayyana yadda ya hallaka sojojin Najeriya

Legas.
Tswirar jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa, ‘yan sanda sun samu rahoton fashewar ne kuma nan take suka tura jami’an kwance bama-bamai (EOD) domin killace yankin da kuma tabbatar da tsaro, in ji Daily Trust.

Ya ce:

“Mun tura jami’an EOD bayan mun samu rahoton fashewar. An killace yankin kuma an gudanar da cikakken bincike.”

Yadda aka dasa bam a jihar Legas

Kwamishinan ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa bam ɗin an dasa shi ne a ƙarƙashin wata mota.

Ya ce an ajiye bam ɗin ne a gefen fasinja na motar, kuma ya fashe ne lokacin da aka kunna injin motar.

"An dasa bam ɗin a ƙarƙashin motar, a gefen fasinja kuma ya fashe ne lokacin da aka kunnata,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa mutum guda ne ya samu rauni a lamarin, kuma an kai shi asibiti inda yake karɓar magani cikin kwanciyar hankali.

Yan sanda sun fara binciken kwakwaf

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

Tijani ya ce bayan cikakken binciken da jami’an kwance bama-bamai suka gudanar, ba a gano wani ƙarin bam a yankin ba.

Ya bayyana cewa an tattara ragowar bam ɗin domin gudanar da binciken kwakwaf yayin da bincike ke ci gaba, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.

IGP Disu.
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kwamishinan ya buƙaci mazauna jihar su kwantar da hankalinsu tare da yin watsi da jita-jitar da ke yaɗuwa cewa tsaro ya tabarbare a Legas.

Ya kuma sake jaddada aniyar rundunar ‘yan sanda ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar, yana gargadin masu aikata laifuffuka da su guji Legas.

Bam ya halaka yan sanda a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa jami’an rundunar ’yan sanda uku sun rasa rayukansu yayin da motarsu ta taka bam kuma ya tashi da su a jihar Zamfara.

Mai taimaka wa gwamnan jihar Zamfara kan harkokin yada labarai, Mugira Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Lamarin ya faru ne lokacin da suka fito sintiri a titin Anka zuwa Bagega kuma jami’an da suka mutu kwararru ne a fannin lalata bama-bamai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262