Manyan Labarai A Yau
Wasu ‘yan daba sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, bayan ziyararsa fadar Ataoja na Osogbo, lamarin da ya jawo musayar harbe-harbe.
Daraktan UNIMEDTH, Farfesa Michael Gbala, ya yi gargadin cewa jabun magunguna na iya kashe mutane fiye da ’yan bindiga, tare da kira da a ƙara sa ido kan ingancinsu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Najeriya daga hutun makonni biyu, kwanaki biyu kafin ranar da aka tsara zai dawo daga hutun da ya tafi.
Dan takarar da ke neman kujerar majalisar wakilai a jihar Katsina, ya ziyarci kauyukan da 'yan bindiga suka kai hare-hare domin jajantawa mutane.
PHIMA ta rufe cibiyoyin lafiya masu zaman kansu 37 a Kano cikin watanni 18 saboda karya ƙa’idoji, yayin da sama da cibiyoyi 1,405 ke da rajista a jihar.
INEC ta yi hasashen adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya zai haura miliyan 100 gabanin zaɓen 2027, yayin da hukumar ke shirin inganta wayar da kan masu zaɓe.
Sojojin Iran sun gargadi kasashen Gulf da kada su taimaka wa sojojin Amurka a yakin da take yi, suna cewa hakan zai sa su zama masu hannu a hare-haren.
Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga bayan an yi musayar wuta. 'Yan sandan sun kuma cafke wasu mutane da dama.
Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa hukumar za ta kasance tsaka-tsaki a zaben 2027 ba tare da fifita kowace jam’iyya ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari