Zargin Bata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Kai Malamin Addini Kara Kotu, Zai Nemi N10bn

Zargin Bata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Kai Malamin Addini Kara Kotu, Zai Nemi N10bn

  • 'Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi barazanar shigar da kara kan Primate Elijah Ayodele
  • Sanata Kwankwaso ya yi barazanar shigar da karar ne kan malamin addinin saboda zargin bata masu suna da kimarsa ta siyasa
  • Madugun na Kwankwasiyya ya ce Primate Ayodele ya yi kalamai wadanda suke na cin mutunci ne a gare shi da kuma kimarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi barazanar shigar da ƙarar ɓata suna da neman har Naira biliyan 10 kan Primate Elijah Ayodele, wanda ya kafa kuma shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church.

Sanata Rabiu Kwankwaso, ta hannnun lauyoyinsa, Magaji Mato Ibrahim SAN & Co, ya zargi malamin addinin da yin kalamai na ƙarya, na ƙeta kuma munana waɗanda za su iya lalata mutuncinsa da gaskiyarsa ta siyasa.

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

Kwankwaso ya yi barazanai kai Ayodele kara kotu
Primate Elijah Ayodele da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 11 ga Yuni, 2026 wadda Saifullahi Hassan, hadimin Kwankwaso kan yaɗa labarai ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026.

Me Kwankwaso yake zargin Ayodele da shi?

Lauyoyin sun ce hankalin wanda suke wakilta ya karkata ga wata wallafa da ta bazu ko dina wadda ake zargin malamin addinin ne ya yi ta kuma ta yadu a shafukan sada zumunta da ma kafofin yaɗa labarai na gida da na ƙasashen waje.

Wasiƙar ta yi zargin cewa Ayodele, yayin da yake jawabi ga mabiya cocinsa a cikin wani wa'azi da aka naɗa kuma aka rarraba shi kai-tsaye a yanar gizo, ya yi kalamai da ke nuna cewa Kwankwaso ba shi da gaskiya a cikin dangantakarsa da Peter Obi kuma an ba shi kuɗi ne domin ya zama abokin takararsa.

Kara karanta wannan

2027: Kwankwaso ya tsallake NDC, ya sayi fam din takara a jam'iyyar PRP? Gaskiya ta fito

A cewar lauyoyin, Ayodele ya ce, “Kwankwaso na bogi ne ga Obi, Kwankwaso zai ci amanarka. An biya Kwankwaso ne domin ya zama mataimakin shugaban ƙasa ga Obi”.

An zargi malami da bata sunan Kwankwaso

Lauyoyin sun bayyana cewa waɗannan kalamai kai-tsaye sun taba amincin wanda suke wakilta, gaskiyar manufarsa, da kuma mutuncinsa na siyasa.

“Wannan wallafa tana nuni ne kai-tsaye kuma babu shakka ga wanda mu ke wakilta kuma tana kai hari ga amincinsa, gaskiyar manufarsa, da mutuncinsa na siyasa a matsayinsa na Ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma abokin takarar Peter Obi a ƙarƙashin jam'iyyar siyasa ta NDC” in ji wasiƙar.

A cewar lauyoyin, wallafar da ake zargin an yi ta ne da nufin ɓata sunan da Kwankwaso ya gina tsawon shekaru kuma ta samar da rarrabuwar kai tsakanin mambobi da magoya bayan jam'iyyar NDC.

Kwankwaso ya yi barazanar shigar da kara
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Lauyoyin Kwankwaso sun bukaci Ayodele ya janye kalamansa

Mato Magaji Ibrahim wanda babban lauya ne da ya kai matakin SAN shi ne wanda tsohon gwamna ya dauko hayarsa domin ya tsaya masa idan ta kama a kotu.

Lauyoyin sun buƙaci Ayodele da ya janye waɗannan kalamai na zargin ɓata suna baki ɗaya a hukumance tare da buga takardar ban-haƙuri a cikin sa'o'i 24.

Kara karanta wannan

Rarara ya zargi Kwankwaso da jefa Najeriya cikin halin kunci, ya kawo dalili

Hakazalika, lauyoyin sun yi gargaɗin cewa rashin biyan waɗannan buƙatu zai janyo ɗaukar matakin shari'a.

Rarara ya yi zargi kan Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya yi zargi kan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rarara ya zargi Kwankwaso da laifin bayar da gudunmawa ga wasu daga cikin kalubalen tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.

Mawakin ya yi zargin cewa Kwankwaso ne ya jefa 'yan Najeriya cikin halin kunci saboda fito da tsarin rike kudaden kananan hukumomi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng