Matatar Dangote Ta Sake Kafa Tarihi a Duniya, Ta Shiga Gaban Amurka a Karo na 2

Matatar Dangote Ta Sake Kafa Tarihi a Duniya, Ta Shiga Gaban Amurka a Karo na 2

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Matatar hamshakin dan kasuwa kuma attajiri lamba daya a Afirka, Aliko Dangote ta sake kafa tahiri wajen jigilar man jirgi zuwa nahiyar Turai
  • Alkaluma sun nuna cewa matatar Dangote ta zarce Amurka, ta zama babbar mai samar da man jiragen sama ga Turai karo na biyu a jere
  • Rahoton kamfanin Kpler ya nuna matatar ta fitar da tan sama da 400,000 na jet fuel zuwa Turai a watan Yulin 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Matatar Dangote ta bayyana cewa ta zarce Amurka wajen zama babbar mai samar da man jiragen sama (jet fuel) ga kasashen Turai karo na biyu a jere.

Matatar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, yana mai cewa wannan nasara ta kara tabbatar da tasirinsa a kasuwannin makamashi na duniya.

Kara karanta wannan

An sanya lokacin bikin auren gata, Gwamna Abba ya yi nasiha ga ma'aurata 1,500

Dangote.
Shugaban rukunin kamfaninin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote da wani bangare da matatar mansa da ke Legas Hoto: Dangote Group
Source: Facebook

Rahoton Kpler ya tabbatar da haka

The Cable ta rahoto cewa bayanan da kamfanin binciken kasuwar kayayyaki na duniya, Kpler, ya tattara, matatar Dangote ta aika da tan sama da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli.

Adadin ya kai kusan kashi 20 cikin 100 na dukkan man jiragen sama da Turai ta shigo da shi a wannan wata.

Kamfanin ya ce hakan ya biyo bayan tan 466,000 da ya fitar a watan Yuni, lokacin da Najeriya ta fara zarce Amurka a matsayin babbar mai samar da wannan man ga Turai.

Dangote na kara tasiri a kasuwar duniya

Kamfanin ya ce ci gaba da samun wannan matsayi ya nuna cewa matatar na iya samar da ingantaccen man jiragen sama da ya dace da ka'idojin kasuwannin duniya.

Rahoton ya nuna cewa Turai ta shigo da kusan tan miliyan 2.06 na kan jrigi a watan Yuli, inda matatar Dangote ta kasance mafi girman mai samar da wannan kaya fiye da Amurka da kasashen Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi zabin Amurka tsakanin sulhu da yaki a Iran

Yawan samar da mai ya karu

Kamfanin ya ce karin fitar da man ya samu ne sakamakon karuwar yawan tace danyen mai, kamar yadda jaridar Bussiness Day ta rahoto.

A watan Yuni, matatar ta loda tan 550,000 na man jirgi daga tashar Lekki, yayin da yawan danyen mai da ake kai mata ya kai ganga 660,000 a rana, wanda shi ne mafi girma tun bayan fara aiki.

Dangote.
Daya daga cikin rumbunan ajiye mai na matatar Dangote da je jihar Legas a Najeriya Hoto: Dangote Group
Source: Facebook

Najeriya na kara zama cibiyar fitar da mai

Babban jami'in gudanarwa na matatar Dangote, David Bird, ya ce baya ga man jiragen sama, kamfanin na fitar da dizal, fetur da sauran kayayyakin man fetur zuwa Turai, Afirka da sauran sassan duniya.

Ya ce hakan na kara tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin kasa mai fitar da ingantattun kayayyakin man fetur da aka tace zuwa kasuwannin duniya.

Dangote ya rage farashin fetur a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Matatar Dangote da ke jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya ta yi sabon rangwame a kan farashin man fetur da dizal.

Kara karanta wannan

Wike zai hana sana'ar acaba da masu adaidaita sahu aiki a birnin Abuja

Sabon sauyin ya nuna an rage farashin fetur da N50 a kowace lita, yayin da aka rage farashin dizal da N80 a kowace lita.

Kamfanin ya ce matakin ya sake tabbatar da kudurinsa na samar da kayayyakin mai masu inganci da araha ga kasuwar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262