Gwamnatin Katsina Ta Yi Magana kan Zargin Daukar Nauyin 'Yan Bindiga zuwa Aikin Hajji

Gwamnatin Katsina Ta Yi Magana kan Zargin Daukar Nauyin 'Yan Bindiga zuwa Aikin Hajji

  • An zargi gwamnatin jihar Katsina da daukar nauyin wasu 'yan bindiga zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji
  • Gwamnatin ta hannun daya daga cikin kwamishinoninta ta fito ta yi martani kan zargin da aka yi a kanta dangane da 'yan bindiga
  • Kwamishinan ya bayyana cewa a shirye gwamnati take wajen bin hanyoyin da doka ta tanada domin daukar mataki kan masu zargin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta yi martani kan zargin cewa ta dauki nauyin kai wasu 'yan bindiga zuwa aikin Hajji.

Gwamnatin ta yi watsi da zargin cewa ta ɗauki nauyin aikin hajjin wasu 'yan bindiga, inda ta bayyana iƙirarin a matsayin na ƙarya wanda ba gaskiya a cikinsa.

An zargi gwamnatin Katsina da daukar nauyin 'yan bindiga zuwa Hajji
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026 a Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki manoma a Kaduna, an kashe bayin Allah

Gwamnatin Katsina kan zargin kai 'yan bindiga hajji

Mu’azu ya mayar da martani ne ga iƙirarin da ake zargin Dr. Bashir Kurfi ne ya yi shi a lokacin wata tattaunawa, inda ya zargi gwamnatin jihar da ɗaukar nauyin 'yan bindiga zuwa aikin Hajji.

Ya ce zargin ba shi da tushe, ba shi da madafa, kuma an yi shi ne da nufin rudar da jama'a, tare da daƙile ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

A cewarsa, wannan iƙirari ya zo ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro, tare da goyon bayan gwamnatin jihar, ke samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da 'yan bindiga da sauran laifuffuka masu alaƙa da hakan.

Ana yunkurin sanya siyasa a harkar tsaro

Kwamishinan ya bayyana zargin a matsayin wani yunƙuri na siyasa da nufin ɗauke hankali daga nasarorin da ake samu wajen magance rashin tsaro.

Ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana da ci gaba da mayar da al'amuran tsaro batun siyasa da wasu mutane da ƙungiyoyi ke yi domin biyan buƙatunsu na kashin kai da na siyasa, rahoton Thisday ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kaddamar da sabon hari Filato, sun hallaka fiye da mutane 15

Nasiru Mu’azu ya yi zargin cewa wasu mutane ba su gamsu da abin da gwamnati ta yi na rashin tallafa wa wasu tsare-tsare da ayyukan da za su iya karkatar da kudaden jama'a daga ayyukan ci gaba.

Gwamnatin Katsina ta musanta zargi kan 'yan bindiga
Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina a ofis Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamnati ta bukaci a kawo hujjoji

Ya ƙalubalanci waɗanda ke da hannu a cikin zargin da su kawo sahihan hujjoji waɗanda za a iya tantancewa domin ƙarfafa iƙirarin nasu.

Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa gwamnati za ta bi dukkan hanyoyi na doka domin kare mutuncinta, sannan ta hukunta duk wanda aka samu yana yaɗa labaran ƙarya da na ɓata suna.

Ya buƙaci mazauna jihar da 'yan Najeriya baki ɗaya da su yi watsi da waɗannan zargi, sannan su ci gaba da marawa hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki baya waɗanda ke aiki domin dawo da zaman lafiya da daidato a jihar.

'Yan bindiga sun kashe babban liman

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka babban limami a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kashe malamin addinin tare da wasu mutane uku, yayin da suka kuma yi garkuwa da wasu mutane daban.

A cewar wata majiya, maharan sun rika shiga gida-gida, suna yin garkuwa da mazauna garin, musamman matan aure a yayin harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng