Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Kashe Babban Limami har da Sace Matan Aure a Sokoto
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauyen jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Hatsabiban 'yan bindigan sun kwashe sa'o'i da dama suna cin karensu babu babbaka yayin harin wanda suka kai da daddare
- An kashe mutane ciki har da babban limamin kauyen tare da sace wasu matan aure a yayin harin da aka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe babban limamin kauyen Kuda-Kuda da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kashe malamin addinin wanda aka gano sunansa Liman Audu tare da wasu mutane uku, yayin da aka yi garkuwa da wasu mutane daban a ranar Alhamis, 24 ga watan Yunin 2026.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce maharan sun afka wa kauyen ne da misalin karfe 12:58 na dare kuma sun kwashe kusan sa'o'i biyu suna cin karensu babu babbaka.
'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
'Yan bindigan sun rika harbe-harbe ba kaukautawa, suka kora dabbobi, tare da sanya mazauna garin tserewa domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce karar harbe-harben ta jefa fargaba a zukatan jama'a yayin da mazauna kauyen suka garzaya domin kwashe iyalansu.
“Muna tsaka da tsaron dare sai kawai muka ji karar harbe-harbe ta bangarori daban-daban. Mun gudu gida, muka tayar da iyalanmu sannan muka tsere zuwa wajen kauyen domin ceton rayukanmu." Inji shi
'Yan bindiga sun rika shiga gida-gida
A cewarsa, maharan sun rika shiga gida-gida, suna yin garkuwa da mazauna garin, musamman matan aure.
“Mutane uku da suka ji rauni an harbe su ne a kirji kuma harsashin ya fito ta bayansu. Yanzu haka da muke magana, an kai su wani asibiti a Sokoto, amma a gaskiya, ba mu da kwarin gwiwa sosai kan yiwuwar ci gaba da rayuwarsu." Inji shi

Kara karanta wannan
Sojoji sun dira maboyar 'yan ta'adda a Katsina, an kashe tantirai da kwato manyan makamai
Majiyar ta bayyana sunayen mamatan da cewa su ne babban liman Liman Audu, Yahaya Hasanu, Zahara Mu'azu da Ibrahim Dayyabu.
Wadanda aka yi garkuwa da su an ce sun hada da Malam Shehu Farar Zaki, Yar Yamma, Khadija da wasu mutane shida daban.
Yadda aka kashe babban limami
Wani mazaunin garin ya tabbatar da kashe-kashen, inda ya ce da farko maharan sun far wa gidan babban limamin ne suka kashe shi kafin su hadu da wasu samari uku tare da umartarsu da su bi su zuwa cikin daji.
“Bayan sun kashe liman, sun hadu da samari uku suka bukaci su bi su. Lokacin da samarin suka ki amincewa, 'yan bindigar sun harbe su tare da kashe su a wurin". Inji shi

Source: Original
'Yan bindiga sun sace iyalan shugaban APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari a gidan shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Yauri a jihar Kebbi.
'Yan bindigan sun kai hari a gidan Alhaji Yusuf Alhassan, inda suka yi awon gaba da matarsa da ɗansa zuwa wurin da ba a sani ba.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tura jami'an tsaro domin bin sawun maharan da suka yi awon gaba da iyalan na shugaban jam'iyyar ta APC.
Asali: Legit.ng
