Nnaji: Tsohon Ministan Tinubu Ya Garzaya Kotun Daukaka Kara bayan An bada Umarnin Kama Shi

Nnaji: Tsohon Ministan Tinubu Ya Garzaya Kotun Daukaka Kara bayan An bada Umarnin Kama Shi

  • Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya ɗaukaka ƙara kan umarnin kotu da ya ba ICPC damar kama shi bisa zargin jabun takardun karatu
  • ICPC ta ce Nnaji ya yi watsi da gayyata da dama da aka aika masa dangane da binciken zargin jabun takardar digiri da ta NYSC
  • A cikin ɗaukaka ƙarar da ya shigar ranar 18 ga Yuni, ya kalubalanci ikon kotun wajen bayar da umarnin kama shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya kalubalanci hukuncin da ya bada umarnin kama shi a kotun daukaka kara.

Tun farko, babbar kotun tarayya ta Abuja ta bai wa hukumar yaki da rashawa ta ICPC umarnin kama tsohon ministan bisa zargin amfani da takardun karatu na digiri da NYSC na bogi.

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

Nnaji.
'Dan takarar gwamnan jihar Enugu karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Uche Nnaji Hoto: Uche Nnaji
Source: Twitter

Yadda aka bada umarnin kama Nnaji

A tsakiyar watan Yunin 2026 ne Premium Times ta ruwaito cewa kotun ta umarci ICPC da ta kama Nnaji domin gudanar da bincike kan zargin jabun takardun karatu da ake yi masa.

Hukuncin ya biyo bayan wata bukata da ICPC ta gabatar a gaban kotun a karkashin shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1160/2026.

Baya ga umarnin kama shi, kotun ta kuma bai wa ICPC damar ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ta hanyar jaridu, kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin yada labarai saboda kin amsa gayyatar hukumar.

Uche Nnaji ya daukaka kara

Nnaji ya daukaka kara a ranar 18 ga Yuni, 2026 kwanaki biyar bayan ya musanta cewa akwai wani umarnin kotu da aka bayar domin kama shi.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Robert Ngwu, ya fitar a ranar 13 ga Yuni, Nnaji ya ce bai boye kansa ba kuma bai taba kauce wa wata hukuma ba.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da shugaban Fulani na Miyetti Allah bayan cafke shi kan $2.5m

Ya kuma ce shi da lauyoyinsa karkashin jagorancin Chief Wole Olanipekun (SAN) ba su taba karbar wata gayyata, sammaci ko wata takarda daga ICPC ba.

Sai dai Premium Times ta bankado cewa wasu takardu da sadarwa tsakanin Nnaji da ICPC sun nuna cewa ya yi watsi da gayyatar da hukumar ta aika masa sau da dama.

Dalilan Nnaji na daukaka karar

A takardar karar da ya shigar, Nnaji ya bayyana rashin amincewarsa da dukkan umarnin da kotun ta bayar.

Ya gabatar da dalilai hudu na kalubalantar hukuncin, inda ya ce kotun ba ta da hurumin bayar da irin wannan umarni na kama shi.

Ya kuma yi zargin cewa kotun ta amince da hujjojin da aka samo ta hanyar na’ura mai kwakwalwa ba tare da cika sharuddan Sashe na 84 na Dokar Shaidu ta 2011 ba.

ICPC.
Hedkwatar hukumar yaki da rashawa ta ICPC da ke Abuja Hoto: ICPC Nigeria
Source: Twitter

Abubuwan da Nnaji ya nema a kotu

Nnaji ya bukaci Kotun Daukaka Kara da ta soke umarnin kama shi tare da yin watsi da karar da ICPC ta shigar a kotun kasa.

Haka kuma ya bukaci a dakatar da aiwatar da umarnin kama shi har sai an kammala sauraron karar daukaka karar da ya shigar.

Kara karanta wannan

Yadda tsohon minista a gwamnatin Tinubu ya yi watsi da gayyatar hukumar ICPC

Tsohon ministan, wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP mai alaka da Nyesom Wike a Jihar Enugu, ya ce idan aka aiwatar da umarnin kama shi, hakan zai hana shi gudanar da yakin neman zabensa.

Yadda Nnaji ya ƙi amsa gayyatar ICPC

A wani rahoton, kun ji cewa taohon ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi watsi da gayyata da dama daga hukumar ICPC.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hukumar ta tura masa gayyatar saboda zargin mallakar takardun bogi na digirin fako da kuma bautar kasa wato NYSC.

Duk da haka, Nnaji ya musanta rahotannin, yana cewa babu wata hukumar ICPC da ke nemansa, tare da zargin gwamnatin Enugu da yada ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262