Tsagin PDP Ya Yi Watsi da Pantami, Ya Gabatar da Dan Takarar Gwamna a Gombe
- Tsagin jam'iyyar PDP ya gudanar da taron mika takardar shaida ga 'yan takarar da suka samu nasara a zaben fitar da gwani
- A wurin taron, an gabatar da takardar shaidar zama dan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe ga Mohammed Yayari
- Hakan na zuwa ne bayan wani tsagin PDP karkashin jagorancin Nyesom Wike ya gabatar da irin wannan takarda ga Farfesa Isa Ali Pantami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsagin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya gabatar da Mohammed Yayari a matsayin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar Gombe.
Wannan yana zuwa ne makonni kaɗan bayan da tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike ya sanar da tsohon Ministan sadarwa, Isa Pantami, a matsayin mai rike da tutar PDP a jihar.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta ce tsagin PDP da ke biyayya ga Turaki ya gabatar da Mohammed Yayari ne yayin wani taro da aka gudanar ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026.
A wurin taron, an miƙa wa 'yan takara na jihohi daban-daban takardun shaidar cin zaɓen fitar da gwani.
Shugabannin jam'iyyar sun yi amfani da damar domin jaddada aminci da sadaukarwa tsakanin masu neman takarar, tare da yin gargaɗi game da sauya sheƙa bayan samun takarar jam'iyya.
PDP za ta kawo sabon tsari
Yayin da yake jawabi a gurin taron, wani fitaccen jigo a jam'iyyar PDP, Ibrahim Turaki, ya bayyana cewa za a buƙaci 'yan takara su sanya hannu a kan rubutaccen alƙawari na dole kafin a miƙa sunayensu ga hukumar zaɓe ta INEC, Vanguard ta kawo rahoton.
“Babu wanda zai ɗauki nasararmu ya kai ta wata jam'iyyar siyasa ta daban sannan ya tsira da hakan."
- Ibrahim Turaki
Ya jaddada cewa za a riƙa tilasta wa 'yan takara masu zuwa nan gaba yin abin da ya dace ta hanyar tsauraran yarjejeniyoyin da aka tsara domin kare buƙatun jam'iyyar.

Source: Facebook
An ba Pantami shaidar samun tikiti
To sai dai kuma, a wani lamarin siyasa na daban da ya gudana a lokaci guda, wani tsagi na jam'iyyar PDP ya kira taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) a Abuja, inda aka gabatar da Pantami a hukumance a matsayin dan takarar gwamnan Gombe.
Taron, wanda shugaban tsagin PDP na ƙasa, Abdulrahman Mohammed ya jagoranta, ya hada shugabannin jam'iyyar da masu ruwa da tsaki daga faɗin ƙasar.
A yayin taron, an miƙa takaddun shaidar cin zaɓen fitar da gwani ga 'yan takarar da ɓangaren ya yi iƙirarin cewa hukumar INEC ta amince da zaɓen nasu kuma ta wallafa su.
PDP ta yi wa APC martani kan Pantami
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi martani kan ikirarin da APC ta yi cewa Farfesa Isa Ali Pantami bai yi murabus daga cikinta ba.
PDP ta yi fatali da ikirarin da jam'iyya mai mulki ke yi cewa ɗan takararta na gwamna, Isa Ali Ibrahim Pantami, har yanzu mamba ne na APC.
Ta bayyana cewa Pantami ya cika dukkan sharuddan doka da kundin tsarin mulki da ake bukata kafin shiga jam’iyyar adawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

