Gwamna Dauda Lawal Ya Amince a Fara Biyan Matasa 'Yan NYSC Alawus a Jihar Zamfara
- Gwamna Dauda Lawal ya amince da biyan alawus ga matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) a jihar Zamfara
- Gwamnatin jihar Zamfara ta ce hakan na nuna kulawarta ga jin dadin matasan da ke yi wa jihar hidima na kowane rukuni na NYSC
- Gwamna Lawal ya umurci Ofishin Akanta Janar da ya fara shirye-shiryen aiwatar da biyan kudaden domin walwalar matasan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da fara biyan alawus da tallafin kudi ga masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke gudanar da aikin bautar kasa a fadin jihar.
A cewar gwamnatin Zamfara, wannan mataki na nuna irin jajircewar Gwamna Lawal wajen kula da walwala da jin dadin matasan da ke bayar da gudunmawa wajen bunkasa bangarori daban-daban na jihar.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar Zamfara, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar yau Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2026.
Rukunin 'yan NYSC da za su amfana
Sanarwar ta bayyana cewa amincewar ta shafi masu yi wa kasa hidima daga na rukunin A Stream I da II har zuwa rukunin C Stream I da II.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin nuna godiya ga kishin kasa, sadaukarwa da gudunmawar da mambobin NYSC ke bayarwa a bangarorin ilimi, lafiya, noma da sauran fannonin da ke da muhimmanci ga ci gaban Zamfara.
Gwamna Lawal ya umarci a fara biya
Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Lawal ya umurci Ofishin Akanta Janar na jihar da ya dauki dukkan matakan da suka dace domin fara biyan kudaden cikin sauki da bin ka’idojin gwamnati.
“Gwamna Lawal ya bayar da umarni ga Ofishin Akanta Janar da ya yi dukkan shirye-shiryen da suka dace domin aiwatar da wannan shiri na bai wa masu yi wa kasa hidima alawus.
"Gwamnatin Zamfara na da kudurin tabbatar da cewa an gudanar da tsarin cikin sauki tare da bin dukkan matakan da aka tanada,” in ji sanarwar.

Source: Twitter
An yaba wa masu yi wa kasa hidima
Gwamnatin Zamfara ta bayyana jin dadinta ga masu yi wa kasa hidima da suka amince su gudanar da aikin bautar kasa a jihar, tare da yabawa da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’umma.
Ta ce za ta ci gaba da daukar matakan da za su inganta walwala da yanayin aiki na matasan da ke yi wa jihar hidima, kamar yadda Punch ta rahoto.
Gwamna Lawal ya kafa tarihi a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Dauda Lawal ya kafa tarihi da ya gina filin jirgin sama na kasa da kasa, irinsa na farko a tarihin jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa an kaddamar da wannan filin jirgi ne a lokacin jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, inda jirgi ya dauki alhazai dag Gusai zuwa Saudiyya.
Gwamnan ya bayyana gina Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa a brinin Gusau a matsayin babban aikin da gwamnatinsa ta aiwatar wanda ya shiga tarihin jihar Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

