Gwamna Abba Ya Bukaci Mutanen Kano Su Sake Zabar Tinubu, Ya Fadi Amfanin Hakan

Gwamna Abba Ya Bukaci Mutanen Kano Su Sake Zabar Tinubu, Ya Fadi Amfanin Hakan

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin dadinsa kan amfanin da jihar ta samu sakamakon hadin gwiwa da gwamnatin tarayya
  • Abba Kabir Yusuf ya bukaci mutanen Kano da su ci gaba da nuna goyon baya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamnan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi aiki tukuru domin fadada hadin gwiwar da ke tsakanin gwamnatinsa da gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da marawa Shugaba Bola Tinubu baya.

Gwamna Abba ya ce shugaban kasar ya cancanci goyon bayan mutanen Kano saboda sadaukarwarsa ga ci gaban jihar da kuma ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Abba ya bukaci a goyi bayan Tinubu
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026 a gidan gwamnati da ke Kano a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya raba wa hadimai filaye da kudi, ya yi magana kan zaɓen Tinubu a 2027

Me Gwamna Abba ya ce kan Tinubu?

Gwamna Abba ya ce mutanen Kano suna da dukkan dalilai na tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan Shugaba Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya lura cewa kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya ta ci gaba da kawo ayyukan ci gaba na a-zo-a-gani ga jihar, musamman a ɓangaren ababen more rayuwa da ayyukan ci gaba.

Gwamna Abba ya yaba wa Tinubu

Gwamna Abba ya jinjina wa Shugaba Tinubu saboda tallafa wa manyan ayyuka a Kano, inda ya bayyana shi a matsayin jagora mai sadaukarwa ga haɗin kan ƙasa, ci gaba, da kuma jin daɗin 'yan Najeriya.

“Ya kamata mutanen Kano su ci gaba da marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ci gaba da kawo ci gaba a jiha da ƙasarmu baki ɗaya. Haɗin gwiwa tsakanin gwamnatinmu da gwamnatin tarayya ya haifar da kyakkyawan sakamako mai amfani ga mutanenmu."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Kara karanta wannan

Ardo Risku: Gwamna ya shirya daukar mataki kan hallaka shugaban Miyetti Allah

Ya yi kira ga shugabannin siyasa, masu ruwa da tsaki, da kuma magoya baya a faɗin jihar da su kasance masu haɗin kai kuma su yi aiki wajen ƙarfafa haɗin gwiwar da ke akwai tsakanin jihar Kano da gwamnatin tarayya.

Gwamna Abba ya yabawa Tinubu
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a wajen taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya taya dan majalisa murna

Gwamna Abba Yusuf ya kuma taya Hon. Shu’aibu Rabi’u Nagogo murna kan nasarar da ya samu a zaɓen cike gurbin da aka gudanar a Kano.

Ya nuna ƙwarin gwiwa cewa sabon ɗan majalisar zai samar da kyakkyawan wakilci kuma zai fafutuka yadda ya dace ga buƙatun mutanen mazaɓar Dawakin Kudu da Warawa aa Majalisar Wakilai.

Gwamnan ya sake jaddada sadaukarwar gwamnatinsa wajen yin aiki tare da Gwamnatin tarayya domin aiwatar da manufofi da shirye-shirye waɗanda za su inganta yanayin rayuwar 'yan ƙasa tare da kawo ci gaba a faɗin jihar.

Ibrahim Sani da ke jihar Kano ya bayyana cewa bai ga dalilin da zai sanya ya sake goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ba.

"Ni dai ban ga dalilin da zai sanya na bada kuri'a ta ga Shugaba Tinubu a zaben 2027 domin bai tabuka komai ba."
"Bamu gani a kasa ba kuma tabbas ba za mu sake bada goyon bayanmu ba. Shi ma da yake maganar mafitarsa yake karewa."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ndume ya gano matsalar da Tinubu ke fuskanta a fadar shugaban kasa

- Ibrahim Sani

Gwamnan Kano ya sauya sunan asibiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauya sunan babban asibitin Dawakin Tofa zuwa Dr Mahmoud Baffa Yola General Hospital.

Gwamna Abba ya yi hakan ne domin karrama marigayi Mahmoud Baffa Yola, dattijon kasa da ya yi fice wajen hidimtawa al’umma da ci gaban jihar Kano.

Ya bayyana cewa marigayin na daga cikin wadanda suka fara bullo da tsarin ilimin manya a jihar Kano, wanda ya ba dubban mutane damar samun ilimi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng