"Ba a Bayar da Mulki"; Shawarar da Wike Ya ba Pantami da Sauran 'Yan Takarar PDP

"Ba a Bayar da Mulki"; Shawarar da Wike Ya ba Pantami da Sauran 'Yan Takarar PDP

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya halarci taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam'iyyar PDP
  • A wurin taron an gabatar da takardar shaidar samun takara ga 'yan takarar jam'iyyar wadanda za su fafata a zaben shekarar 2027
  • Nyesom Wike ya sanar da 'yan takarar cewa mulki ba abu ba ne wanda ake samunsa a kwance, dole sai an tashi tsaye wajen nemansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya buƙaci mambobin jam'iyyar PDP da su shiryawa gagarumin yaƙin siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Wike ya bayyana cewa ba a taɓa bayar da mulki haka kawai, sai dai ana samunsa ne ta hanyar fafutuka, sadaukarwa, da kuma aiki tuƙuru.

Wike ya bayar da shawara ga 'yan takarar PDP
Nyesom Wike na jawabi a wajen taron NEC na PDP a Abuja Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 109 na jam'iyyar PDP, ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya karbi shaidar takarar gwamnan jihar Gombe a babban zaben 2027

A wurin taron dai an gabatar da takardar shaidar samun takara ga 'yan takarar jam'iyyar PDP domin shiga zaben shekarar 2027.

Wace shawara Nyesom Wike ya ba 'yan PDP?

Wike ya shaida wa magoya bayan jam'iyyar cewa siyasar adawa tana buƙatar juriya, tsari, da kuma ƙuduri, inda ya yi gargaɗin cewa jam'iyyar ba za ta koma kan mulki ta hanyar takama ko tunani kawai ba.

Yayin da yake kafa hujja da tasa tafiyar ta siyasa, Wike ya buƙaci masu neman takara da kada su gaza gwiwa saboda matsin lamba, kamu, ko dambarwar shari'a, inda ya bayyana cewa nasarar siyasa galibi ana samun ta ne ta hanyar fuskantar ƙalubale.

“Babu wanda ke bayar da mulki. Mulki nemansa shi ake yi. Dole ne ku yi yaƙi dominsa kafin ku same shi. Babu wanda ke bayar da mulki, kuma babu wanda ya shirya ba da mulki kyauta. Dole ne ku yi fafutuka dominsa. Dole ne ku yi yaƙi dominsa. Kada ku ji tsoro."

- Nyesom Wike

Batun rikicin jam'iyyar PDP

Yayin da yake magana ga cikin gida na jam'iyyar da kuma shari'o'in kotu, Wike ya toge a kan cewa jam'iyyar PDP tana nan daram a kan tafarkinta na shirye-shiryen zaɓe kuma ba za ta bari ƙalubalen shari'a ya tarwatsa tsarinta ba, The Nation ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

"An ci amanarmu": Sanata Maidoki ya yi fallasa kan APC bayan komawa ADC

“A iya sani na, 26 ga watan Yuni shi ne lokacin da za su bayar da lambar sirri ga jam'iyyun siyasa domin sanya sakamakon zaɓen fitar da gwani. Kada ku damu, mun shirya tsaf. Babu wanda ke tsoron kotu; an yi kotuna ne domin mutane, ba domin fatalwowi ba."

- Nyesom Wike

Wike ya ba 'yan PDP shawara
Ministan Abuja, Nyesom Wike na magana da manema labarai Hoto: @Olayinkalere
Source: Facebook

PDP ta ba Pantami takardar shaidar takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya karbi takardar shaidar takara daga hannun jam'iyyar PDP.

Pantami ya karbi takardar ne yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da kuma rantsar da sababbin mambobin NEC na jam’iyyar PDP.

A yayin taron, jam’iyyar PDP ta mika takardun shaidar takara ga wasu daga cikin ‘yan takarar gwamna da aka amince da su tare da wallafa sunayensu a hukumance.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng