An Samu Bakin Fuska da aka Rantsar da Sababbin Sanatoci 4 a Majalisar Dattawa
- Majalisar dattawan Najeriya ta rantsar da sanatoci hudu da suka lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata
- Sababbin sanatocin da suka karbi rantsuwar kama aiki a Majalisar dattawa sun fito ne daga jihohin Ondo, Nasarawa, Enugu da Rivers
- Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya taya su murna tare da yi wa tsofaffin 'yan majalisar da suka rasu addu’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawan Najeriya ta rantsar da sanatoci hudu da suka samu nasara a zabukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, 20 ga watan Yuni, 2026.
Bayanai sun nuna cewa sababbin 'yan Majalisar dattawan za su wakilci mazabun sanatoci daga jihohin Ondo, Nasarawa, Enugu da Rivers.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sanatocin sun maye gurfin tsofaffin wakilan mazabunsu, wadanda suka rasu da wadanda suka ajiye aiki domin karbar wani mukami.

Kara karanta wannan
Yadda matar Janar Rabe ta ki tafiya ta bar shi a daji duk da barazanar 'yan bindiga
Guraben da sanatoci 4 suka maye a Majalisa
Daga cikin wadanda aka rantsar akwai Farfesa Francis Faduyile na jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta Kudu, wanda ya maye gurbin Sanata Jimoh Ibrahim bayan nada shi a matsayin wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.
Haka kuma, Barrista Danladi Halilu Envulu-Anza na APC daga mazabar Nasarawa ta Arewa ya maye gurbin marigayi Sanata Godiya Akwashiki wanda ya rasu a watan Disamban 2025.
Sauran sanatocin sun hada da Asogwa Ikeje Israel na APC daga Enugu ta Arewa, wanda ya maye gurbin marigayi Sanata Okey Ezea da ya rasu a watan Nuwamban 2025.
Sai kuma Olaka Nwogu na jam’iyyar PDP daga mazabar Rivers ta Kudu maso Gabas, wanda ya maye gurbin marigayi Sanata Barry Mpigi da ya rasu a watan Fabrairun 2026.
An yi addu’a ga sanatocin da suka rasu
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya jagoranci zaman majalisar a yau Laraba, 24 ga watan Yuni, 2026, ya yi addu’ar Allah ya jikanci sanatocin da suka rasu.

Kara karanta wannan
INEC ta mika takarda ga 'yan takarar da suka lashe zaben cike gurbi a Kano da wasu jihohi 5
Ya kuma taya sababbin sanatocin murnar samun nasara tare da yi musu fatan alheri a sabuwar tafiyarsu ta wakilcin al’umma.

Source: Facebook
Yawan sanatocin jam’iyyu a majalisa
Bayan rantsar da wadannan sanatocin, a halin yanzu jam’iyyar APC mai mulki tana da sanatoci 88 a Majalisar Dattawa.
Jam’iyyar ADC kuma na da sanatoci tara, PDP na da biyar, NDC na da hudu, yayin da APGA, LP da Accord ke da sanata daya-daya.
Jimillar sanatocin Majalisar Dattawa a halin yanzu ta kai 109 kamar yadda doka ta tanada, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Majalisar dattawa ta nemi a daina sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatocin jihohi su daina kulla yarjejeniyar sulhu da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.
Sanatocin sun bayyana cewa irin wadannan matakai galibi ba sa samar da mafita mai dorewa, sannan suna iya zama hanyar da ke kara karfafa ayyukan ta'addanci.
Haka zalika,Majalisa ta nuna damuwa cewa yawaitar makamai na daga cikin manyan abubuwan da ke kara ta'azzara matsalar tsaro a sassa daban- daban na kasar nan.
Asali: Legit.ng