Manyan Labarai A Yau
Atiku Abubakar ya ce ya taba ceto rayuwar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidan yari ta hanyar tona wani shirin allurar da ya yi zargin za ta iya kashe shi.
Birtaniya ta hana ’yan kasarta tafiya wasu sassan jihohin Najeriya 11 saboda matsalar tsaro, yayin da Abuja da wasu jihohi 19 ke ƙarƙashin shawarar yin tafiya.
Dan Majalisar Amurka, Riley Moore ya dace cewa kasarsa ba za ta sauya matsayarta kan zargin tauye hakkin addini da take zargin ana hi a Najeriya.
Mai girma Bola Tinubu ya bukaci Adeleke ya guji wulakanta abokan hamayyarsa bayan nasarar zaben Osun, yana cewa bai ci wani mutum ba, ya ci zabe ne.
Segun Sowunmi ya yi gargadin cewa Tinubu na iya fuskantar zargin magudin zaɓe ko da ya yi nasara a 2027, yana kira ga ’yan siyasa su mutunta sakamakon zaɓe.
Kimanin mutane 40 ne ake tunanin sun mutu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da manoma ya kife a Gorau, karamar hukuma Goronyo, Jihar Sokoton Najeriya.
Atiku Abubakar ya ce ba zai sake neman takarar shugaban ƙasa ba idan ya sha kaye a zaɓen 2027, tare da kira ga masu katin zaɓe su fito su kada kuri’a.
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi watsi da sabon shirin takunkumin tattalin arziki na Trump, yana mai cewa zai kara jefa Amurka cikin rashin nasara.
Tsohon gwamnan jihar Cross Rives, Donald Duke, ya bayyana gargadin da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Olusegun Obasanjo kan Atiku Abubakar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari