Halin Matsi Na Damun Tinubu, Ya Fadi Hanyar Tsame Mutane Miliyan 5 Daga Talauci

Halin Matsi Na Damun Tinubu, Ya Fadi Hanyar Tsame Mutane Miliyan 5 Daga Talauci

  • Gwamnatin Tarayya ta ce shirinta na koyar da sana’o’i da ƙarfafa matasa zai taimaka wajen fitar da ’yan Najeriya daga talauci
  • Shirin da ake aiwatarwa ƙarƙashin NPRGS ya fara ne a Abuja, kafin a kai shi Oyo da sauran jihohi da yankunan ƙasar
  • Matasa 200 ne suka fara samun horo a Oyo kan zane da AI, kwalliya da ɗinkin zamani, yayin da za a raba kwamfutoci da kayan sana’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ce shirye-shiryenta na koyar da sana’o’i da ƙarfafa matasa an tsara su ne domin dakile talauci.

Gwamnatin Tinubu ta shirya fitar da matasan Najeriya miliyan biyar daga talauci da kuma samar da hanyoyin samun abin dogaro mai ɗorewa.

Tinubu ya shirya tsamo yan Najeriya daga kangin fatara da suke ciki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Dr Abiola Arogundade, Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Ilimin Fasaha, Sana’o’i da Kasuwanci, OSSAP-TVEE, wadda ke jagorantar shirin, ta bayyana haka a Ibadan, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta samar wa matasan Najeriya ayyuka a ƙasashen waje, an ji yadda tsarin yake

Yadda Tinubu ta shirya yaki da talauci

Shirin da ake aiwatarwa ƙarƙashin Tsarin Rage Talauci da Samar da Ci Gaba na Ƙasa, wato NPRGS, yana da nufin bai wa matasa dabarun sana’o’i masu amfani da kuma dacewa da bukatun kasuwa.

Hakan zai taimaka wajen ƙarfafa ’yancin kai ta fuskar tattalin arziki da kuma inganta damar matasa wajen samun ayyukan yi, musamman a fannonin da ake samun ƙarin buƙata.

Arogundade ta bayyana hakan ne yayin fara matakin shirin a Jihar Oyo, wanda zai gudana daga ranar 28 ga Satumba zuwa 9 ga Oktoba.

Ta ce shirin ya fara ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja, kafin a kai shi Jihar Oyo, kuma daga bisani za a faɗaɗa shi zuwa sauran jihohi da yankunan siyasar ƙasar.

A ƙarƙashin matakin shirin na Jihar Oyo, matasa 200 ne ke samun horo a fannonin zane da basirar wucin gadi, wato AI, kwalliya da ɗinkin zamani.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya fada wa 'yan Arewa muhimmancin goyon bayan Tinubu

An fara horas da matasa a Najeriya
Taswirar jihar Oyo da aka fara horas da matasa domin yaki da talauci. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka rarraba matasa domin koyon sana'a

Daga cikin waɗanda ake horaswa, mutum 30 na koyon zane-zane da AI, yayin da mutum 85 ke samun horo kan sana’ar kwalliya, wasu 85 kuma kan ɗinkin zamani, cewar Daily Post.

Arogundade ta ce shirin bai tsaya ga koyar da sana’a kawai ba, domin za a haɗa waɗanda suka amfana da ƙungiyoyi da damar kasuwanci domin taimaka musu wajen samun hanyoyin dogaro da kai.

Ta ce:

“Da wannan shiri, muna horas da mutane 200. Haka kuma, za mu raba kwamfutocin hannu guda 500 a babban bikin kammala shirin, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa amfani da fasahar zamani.”
“Muna ƙarfafa mutane 700 kai tsaye ta wannan shirin, kuma hakan zai haifar da ƙarin masu amfana, ina so kawai in ƙarfafa su da su yi iya ƙoƙarinsu. Ina so su sani cewa Shugaba Bola Tinubu yana tunanin dukkan ’yan Najeriya, musamman matasa, kuma yana shirye ya magance matsalolinsu.”

Kara karanta wannan

Kaico: Abin da ya faru wanda ya kai ga kashe babban malamin jami'ar ABU, ya ba da wasiyya

Babbar hadimar shugaban ƙasar ta sake jaddada ƙudurin Gwamnatin Tarayya na samar da damarmaki ga matasa domin su dogara da kansu ta fuskar tattalin arziki, ta hanyar koyar da sana’o’i domin yaki da talauci.

Fatara: Tinubu ya shawarci yan Najeriya

A wani labarin, an ji cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya kan abin da ya kamata su runguma domin yaki da fatara.

Shugaban ya ce duk da cewa ana fama da talauci amma akwai abubuwan da idan ba a nisance su ba za su kara damuwa ga Najeriya.

Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin da shugabannin majalisar tarayya suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Tags: