'Yan Bindiga Dauke da Makamai Sun Yi Ta'addanci bayan Kai Hari a Kaduna
- ’Yan bindiga dauke da makamai sun kashe jami’in tsaro na JTF a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yamma
- Harin ya faru da misalin ƙarfe 11 na dare a Kyauta New Millennium City da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
- Jami'an tsaro na 'yan sa-kai sun bi sawun maharan wadanda suka zo suka aikata ta'asa kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - ’Yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar hadin gwiwa (JTF), tare da yin garkuwa da wata mata mai suna Asma’u da ɗanta Umar, jihar Kaduna.
'Yan bindigan sun yi ta'asar ne a Kyauta New Millennium City da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Talata, 18 ga watan Agustan lokacin da maharan suka shiga cikin garin tare da yin awon gaba da matar da ɗanta.
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Kaduna
An tattaro cewa mijin Asma’u ya tsira daga harin ne bayan ya ɓuya a cikin motarsa yayin da ’yan bindigar ke gudanar da farmakin.
Wani jami’in JTF da ya yi magana bisa sharadin sakaya sunansa, ya ce jami’an tsaron sa-kai sun kwashe dare suna ƙoƙarin gano inda maharan suka nufa.
“An yi garkuwa da wata mata da ɗanta, amma mahaifin ya samu damar tserewa yayin harin. An harbi ɗaya daga cikin jami’an JTF ɗinmu kuma ya rasu a asibiti,” in ji shi.
An tattaro cewa an harbi jami’in JTF ɗin ne a kansa yayin harin, sannan aka garzaya da shi zuwa asibitin Barau Dikko Specialist Hospital da ke Kaduna domin yi masa magani. Sai dai rahotanni sun ce ya rasu ne bayan shafe wasu sa’o’i da isa asibitin.
Wani babban jami’in tsaro, wanda ya yi magana bisa sharadin sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin yin magana kan lamarin ba, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici.
'Yan sanda ba su ce komai ba
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Ba a samu damar tuntuɓar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansur Hassan, ta waya domin jin ta bakinsa ba.
Har zuwa lokacin haɗa rahoton, ba a san inda Asma’u da ɗanta Umar, waɗanda aka yi garkuwa da su, suke ba.

Source: Facebook
Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an tsaro sun hallaka akalla ‘yan bindiga 24 bayan sun dakile yunkurin sace mutane a jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun dakile yunkurin 'yan bindigan ne na sace mazauna kauyen Gidan Bawa da ke gundumar Kandarawa, karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng

