Tsohon Gwamna Ya Rasu a Najeriya, Majalisar Tarayya Ta Karrama Shi
- Majalisar Dattawa ta karrama tsohon gwamnan Kogi, Ibrahim Idris, wanda ya rasu a Landan ranar 20 ga Satumba yana da shekaru 77
- Sanata Jibrin Isah ya ce Idris ya taka muhimmiyar rawa a kasuwanci, siyasa da hidimar jama’a, tare da barin manyan ayyuka a Kogi
- Majalisar ta yi shiru na minti guda domin karrama marigayin, yayin da Sanatoci suka bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalansa da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar Dattawa ta Najeriya ta yi zaman makoki kan rasuwar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, wanda ya rasu a Landan ranar 20 ga Satumba 2026.
An gabatar da kudirin gaggawa ne karkashin jagorancin Sanata Jibrin Isah, wanda ya bayyana Idris a matsayin fitaccen ɗan Najeriya mai muhimmiyar gudunmawa ga kasuwanci, siyasa da hidimar jama’a.

Source: Facebook
Takaitaccen tarihin marigayi tsohon gwamnan Kogi
An haifi Idris ranar 6 ga Afrilu 1949 a Idah, Jihar Kogi, sannan ya yi wani bangare na yarintarsa a Onitsha, Jihar Anambra, inda mahaifinsa ke kasuwanci, cewar Vanguard.
Ya halarci Holy Trinity Primary School da ke Onitsha, da kwalejin Prince Commercial da ke Buguma, Jihar Rivers, kafin ya samu digirinsa na farko daga Jami’ar Abuja.
Kafin shiga siyasa, Idris ya kafa babbar daular kasuwanci karkashin kamfanin Ibro, wanda ya shafi gine-gine, kera kayan daki, masana’antu da harkar otal.
Daga cikin manyan kasuwancinsa akwai Ibrahim Furniture Factory da ke Sokoto da kuma Ibro Hotel, daya daga cikin otal-otal na farko a yankin.
Daga bisani aka zabi Idris a matsayin gwamnan Jihar Kogi karkashin jam’iyyar PDP, inda ya yi mulki daga 29 ga Mayu 2003 zuwa 6 ga Janairu 2012.
Hakan ya sanya shi zama gwamnan farar hula da aka zaba mafi dadewa a tarihin Jihar Kogi.
Sanata Jibrin ya ce gwamnatin Idris ta gudanar da manyan ayyukan more rayuwa, musamman a Lokoja, ciki har da gidajen ma’aikata da gine-ginen azuzuwa.

Source: UGC
Sanatoci sun yabawa marigayi Ibrahim Idris
Tsohon gwamnan Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya yaba da gudunmawar Ibrahim Idris ga Jihar Sokoto, inda ya kafa kasuwancinsa tare da renon iyalansa.
Tambuwal ya ce Idris, wanda aka fi sani da Ibro, ya fara harkar kasuwanci ne a masana’antar katako kafin ya fadada zuwa harkar otal.
Ya ce marigayin ya kasance mutum mai matukar daraja a Sokoto, inda Sarkin Musulmi ya karrama shi da sarautar “jakada”.
Sanata Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa ya bayyana Idris a matsayin jagoran da ya himmatu wajen kyautata rayuwar jama’a.
Oshiomhole ya tuna yadda tsohon gwamnan ya nuna shirye-shiryen biyan ma’aikata mafi karancin albashi a lokacin da yake kan mulki.
Gwamna Ododo ya kadu da rashin Idris
An ji cewa Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamna, Alhaji Ibrahim Idris, yana da shekaru 77 a wani asibiti da ke Birtaniya.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku tare da sanar da jana’izar gwamnati ga marigayin.
Idris ya shugabanci jihar Kogi daga 2003 zuwa 2012, inda ya kasance gwamnan da ya fi dadewa a kan mulki a jihar.
Asali: Legit.ng


