"Na Tausaya Masa": Jigon PDP Ya Hango Matsalar da Za Ta Tunkari Tinubu idan Ya Yi Tazarce
- Tsohon kakakin PDP, Segun Sowunmi, ya yi gargadi kan matsalar da Shugaba Bola Tinubu zai iya fuskantar idan ya yi nasara a zaben 2027
- Sowunmi ya ce babban kalubalen Najeriya ba wai wanda zai lashe zaben ba ne, sai yadda ’yan siyasa da magoya bayansu za su karɓi sakamakon
- Ya bukaci ’yan siyasa su nemi hakkinsu ta hanyoyin doka idan suna ganin an tafka magudi a zaben da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Segun Sowunmi, ya yi gargadi kan nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Sowunmi ya yi gargadin cewa Shugaba Bola Tinubu na iya fuskantar zargin magudin zabe bayan zaben shugaban kasa na 2027 ko da ya yi nasara.

Source: Facebook
Wane kalubale Tinubu zai fuskanta?
Sowunmi ya bayyana hakan ne yayin da yake tantance damar Tinubu ta sake lashe zaben shugaban kasa na 2027 a shirin Politics Today na Channels Tv.
Ya ce babban kalubalen da Najeriya za ta fuskanta ba wai tantance wanda ya yi nasara ko wanda ya sha kaye a zaben ba ne, sai yadda jam’iyyu, ’yan takara da magoya bayansu za su karɓi sakamakon.
“Ina tausaya masa (Tinubu) domin bayan ya yi nasara, za su fara cewa ya yi magudi,” in ji Sowunmi.
Karɓar sakamakon zabe
Sowunmi ya jaddada cewa yadda ’yan siyasa za su karɓi zabin masu kada kuri’a zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan zaben.
A cewarsa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ’yan kasa ikon zabar shugabanninsu ta hanyar kada kuri’a, don haka ya kamata ’yan siyasa su mutunta sakamakon zaben ko da bai yi musu dadi ba.
“Babban kalubalen da ke gaban zaman lafiyar kasar nan a gaba ba wai wanda zai yi nasara ko wanda zai sha kaye ba ne, sai yadda za su karɓi sakamakon.” In ji shi.
Sowunmi ya ce zabe na iya samar da sakamakon da ya saba da abin da dan takara ko jam’iyya ke tsammani, amma hakan kadai bai kamata a dauke shi a matsayin hujjar cewa an tafka magudin zabe ba.
“Saboda idan ka gudanar da zabe kuma mutane suka iya kada maka kuri’a, za su iya kada kuri’a ga abokin hamayyarka,” in ji shi.
Gargadi kan tayar da hankali
Ya yi gargadin cewa ci gaba da kin amincewa da sakamakon zabe da kuma kokarin tayar da hankalin jama’a kan wanda aka ayyana a matsayin wanda ya yi nasara na iya kawo barazana ga zaman lafiyar kasa.
Ya bukaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su sanya muradun kasa a gaba fiye da bukatun jam’iyya.
Ya kuma jaddada cewa ’yan takarar da suka yi imanin cewa an yi wa zaben katsalandan ya kamata su nemi hakkinsu ta hanyoyin da doka da kundin tsarin mulki suka tanada.
Sowunmi ya ce zaman lafiyar dimokuradiyyar Najeriya zai dogara ne ba kawai kan sahihancin zaben 2027 ba, har ma da yadda ’yan siyasa za su amince da halastaccen sakamakon zabe tare da warware sabanin da ya taso ta hanyoyin doka.

Source: Facebook
An yi hasashen faduwar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi hasashen faduwar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa idan aka yi sahihin zabe, kafin karfe 4:00 za a kayar da tsohon gwamnan na jihar Legas.
Asali: Legit.ng


