Tirkashi: ICPC Ta Sake Bankado Wata Hukumar Bogi, Shugaba Tinubu Ya Ba da Umarni

Tirkashi: ICPC Ta Sake Bankado Wata Hukumar Bogi, Shugaba Tinubu Ya Ba da Umarni

  • Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta kama Prince George Buchi Nwabueze bayan gano wata hukuma da ake zargin ta bogi ce a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
  • ICPC ta gano hukumar ta National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office a yayin binciken wata hukumar bogi da ake zargin Adeyemi Matthew ya tafiyar da ita
  • Shugaba Tinubu ya kuma dakatar da manyan sakatarorin uku kan lamarin da ya shafi hukumar bogin da aka gano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta kama Prince George Buchi Nwabueze dangane da gano wata hukumar da ake zargin bogi ce, mai suna National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta gano hukumar a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.

Kara karanta wannan

Malamin addini da ke goyon bayan Tinubu ya magantu kan tallafin mai

ICPC ta bankado hukumar bogi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugaban hukumar ICPC Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban ICPC, Dr Musa Adamu Aliyu (SAN), ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayani bayan ganawa da Shugaba Tinubu a ranar Juma’a, 21 ga watan Agustan 2026.

Yadda aka gano hukumar

Dr Musa Aliyu Adamu ya ce an gano sabuwar hukumar bogin ne a wani ɓangare na binciken da ake ci gaba da gudanarwa kan wata hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

Ya ce Adeyemi Matthew ne ya kasance yana tafiyar da hukumar ta Presidential Foreign Intervention Promotion Council.

Shugaban ICPC ya ƙara da cewa an ware wa sabuwar hukumar wani ofishin aiki ba bisa ƙa’ida ba a cikin harabar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Ana ci gaba da bincike

Ya ce an gano lamarin ne yayin da hukumar ke gudanar da wani babban bincike da Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a yi tun da farko, inda aka gano wanda ya shirya hukumar bogin, wato Prince George Buchi Nwabueze, wanda aka gano yana amfani da sunaye daban-daban.

Kara karanta wannan

Dalibar BUK ta shiga matsala da ta taba 'kimar' hukumar EFCC

Aliyu ya ce an gano cewa wanda ya kafa hukumar yana kuma amfani da wasu nau’o’in sunansa guda huɗu, wato George Nathan, George Nathan Nwabueze, Honourable George Buchi Nwabueze, Prince George Buchi Nwabueze da George Nwabueze.

Ya bayyana cewa ICPC ta tuntubi Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da muhimman bayanai da suka shafi hukumar bogin da ake bincike a kanta, sannan ta yi wa Shugaban Ƙasa cikakken bayani kan sababbin abubuwan da aka gano.

“Na yi wa Mai Girma Shugaban Ƙasa cikakken bayani kan waɗannan sababbin abubuwan da suka faru. ICPC za ta ci gaba da bincikenta yadda ya kamata,” in ji shi.

Tinubu ya dakatar da sakatarori

Baya ga umarnin kama Nwabueze, Shugaba Tinubu ya kuma umarci a dakatar da manyan sakatarori uku kan lamarin.

Manyan sakatarorin da Shugaba Tinubu ya umarci a dakatar su ne M.S Danjuma, Injiniya Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah.

El-Rufai ya kai karar hukumar ICPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙarar N10bn kan hukumar ICPC.

El-Rufa'i ya garzaya kotu ne bisa zargin cewa jami'an hukumar sun hana matarsa da ɗansa damar ganinsa yayin da yake tsare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng