An Samu Kokon kan Mutane da Kasusuwa a Sansanin 'Yan Ta'adda
- Rundunar ’yan sandan Abia ta ce jami’anta sun gano kokon kan mutum 28 da wasu kasusuwa a wasu sansanonin da ake zargin ’yan ta’adda ne
- An gano gawarwakin ne yayin wani samame da rundunar ta kai sansanonin da ke cikin dazuzzukan Umuaku da Nneato a ƙaramar hukumar Umunneochi
- ’Yan sandan sun ce mutanen da ke sansanonin sun tsere bayan jami’an tsaro sun isa wurin, inda aka fara bincike domin gano gawarwakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abia – Rundunar ’yan sandan jihar Abia ta ce ta gano kokon kan mutane 28 da wasu kasusuwa a wasu sansanonin da ake zargin miyagu ne a dazuzzukan Isuochi, ƙaramar hukumar Umunneochi.
Rundunar ta ce an gano gawarwakin ne yayin wani samame da jami’an rundunar suka kai sansanonin Umuaku da Nneato, Isuochi.

Source: Twitter
Wajen da aka kai samame
Jami’an Rundunar Yaki da Munanan Laifuka, Yaki da Satar Mutane, Yaki da Kungiyoyin Asiri, Sashen Leken Asiri da Rapid Response Squad ne suka gudanar da samamen tare da jami’an ofishin ’yan sanda na Isuochi.
Kakakin rundunar, DSP Maureen Chinaka, ta ce samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu a karkashin shirin rundunar na kai samame.
Ta ce da isar jami’an tsaron sansanonin, waɗanda ake zargin miyagun ne suka tsere zuwa cikin dajin, inda suka bar sansanonin babu kowa.
An gano kokon kan mutane
Chinaka ta ce jami’an sun gano kwanyar mutane 28 da wasu kasusuwa da ake zargin na mutanen da aka sace ne.
The Sun ta rahoto ta ce rundunar ta fara bincike domin gano waɗanda gawarwakin suke da kuma tantance yanayin da ya kai ga mutuwarsu.
Rundunar ta kuma ce tana ci gaba da sanya ido a yankin tare da ƙara ƙoƙarin kamo waɗanda suka tsere.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun bi dare, sun kama tare da kashe sakataren harkokin lafiya a Katsina
Kiran jama’a da su taimaka
Kwamishinan ’yan sandan jihar Abia, CP Wilfred Afolabi, ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da suka dogara da bayanan sirri domin dakile ayyukan miyagu a jihar.
Afolabi ya ce Abia za ta ci gaba da kasancewa wurin da masu aikata laifi ba za su samu mafaka ba, tare da kira ga mazauna jihar da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suka ga yana da alaƙa da aikata laifi.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da aikata laifuka a jihar.
An kashe matar aure a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kashe Aishatu Salisu, mahaifiyar ’ya’ya biyar, a wani yunkurin kwace wayarta a gidanta da ke unguwar Wuro Shi'e a Gombe.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:35 na asubahin ranar Asabar, lokacin da wasu da ake zargin maharan ne dauke da adduna da makamantansu suka kutsa gidan Inspector Salisu Waziri.
Wani ɗan gidan, Usman Ismaila, ya ce mutuwar Aishatu ta jefa ’yan uwa da abokanta cikin jimami. Kakakin ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya ce maharan sun yi yunkurin kwace wayarta.
Asali: Legit.ng
