2027: Kalubalen da Ke gaban Akpabio, Barau Jibrin da Shugabannin Majalisa
Shugabannin Majalisar Tarayya ta Ƙasa sun fara fuskantar sababbin ƙalubalen siyasa yayin da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisa na 2027 ke gabatowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabannin majalisar tarayya a Najeriya na shirin fuskantar kalubale a siyasa gabanin zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya na ranar 16 ga Janairu 2027.
Yayin da da dama daga cikin manyan jami’an majalisar suka samu tikitin jam’iyyunsu, wasu sun fadi a zaɓen fitar da gwani.

Source: Facebook
Wasu daga cikin waɗannan shugabannin majalisar, waɗanda suka shafe shekaru a majalisar, za su fafata da manyan ’yan takara da ke neman kujerunsu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
1. Godswill Obot Akpabio - Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Godswill Obot Akpabio shi ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya na 15, kuma yana wakiltar Mazabar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Akpabio ya yi murabus daga shugabancin marasa rinjaye a shekarar 2018, bayan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, daga PDP.
A zaɓen 2027, ɗan takarar ADC, Pat Ibanga, zai ƙalubalanci Akpabio, kuma ita ce matar ɗan’uwansa, Ibanga Akpabio.
Haka kuma zai fafata da tsohon babban mataimakinsa kan harkokin majalisa, kuma tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Patty Etete, wanda ke takara ƙarƙashin NDC.

Source: Facebook
2. Abbas Tajudeen - Kakakin Majalisar Wakilai
A Majalisar Wakilai, Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen, wanda ke wakiltar Mazabar Tarayya ta Zaria a Kaduna ƙarƙashin APC, na neman wa’adi na biyar a jere.
Gabanin zaɓen 2027, Abbas ya samu tikitin APC na Mazabar Tarayya ta Zaria ba tare da hamayya ba a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.
Idan ba a samu wani sauyi ba, manyan abokan hamayyarsa sun haɗa da Suleiman Ibrahim Dabo na ADC da Hamisu Idris, wanda aka fi sani da Alhajin Ganda, na NDC.

Source: Twitter
3. Barau Jibrin - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Barau I. Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa, shi ma ya samu tikitin sake neman kujerarsa a 2027.
Yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa, Barau zai fuskanci hamayya daga Saleh Shehu Kwidawa na ADC da Nasiru Sule Garo na NDC, cewar Punch.
Kwidawa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ne, yayin da Garo ɗan’uwan Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, kuma surukin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ne.
4. Benjamin Kalu - Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai
Benjamin Okezie Kalu shi ne Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, yana wakiltar Mazabar Tarayya ta Bende a Jihar Abia ƙarƙashin tutar APC.
Kalu lauya ne kuma ɗan siyasa, kuma ya samu tikitin APC na neman wa’adi na uku a Bende bayan ya fito ba tare da hamayya ba a zaɓen fidda gwani na Mayu.
Daga cikin manyan ’yan takarar kujerar akwai Chimaobi Anyaso na LP, da tsohon ɗan wasan Super Eagles, Karibe Ojigwe, na NDC.

Source: Facebook
5. Usman Bello Kumo - Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai
Usman Bello Kumo yana wakiltar Mazabar Tarayya ta Akko a Jihar Gombe, kuma shi ne Babban Mai Bulala na Majalisar Wakilai ta Ƙasa.

Kara karanta wannan
Nasarar Atiku Abubakar a zaben 2027 na iya jawo matsala mai girma tsakanin Kudu da Arewa
Shi ɗan majalisa ne mai wa’adi uku, inda ya wakilci mazabar a Majalisun Dokoki na 7 da 9, kuma a halin yanzu yana Majalisa ta 10.
A zaɓen 2027, Kumo ya samu tikitin APC domin neman wa’adinsa na huɗu a matsayin ɗan Majalisar Wakilai.
Daga cikin ’yan takarar da za su fafata da shi akwai Bashir Abdullahi Gaddafi na ADC da Alhaji Gidado Lawanti na PDP.
A wannan makon, Sanata Danjuma Goje ya bukaci masoyansa da ka da su zabi makiyansa a APC wanda ake da tabbacin cewa akwai Hon. Kumo a ciki.

Source: Facebook
2027: Pantami da wadanda ka iya samun matsala
Mun ba ku labarin cewa hukuncin Kotun Ƙoli kan wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 ya jefa takarar wasu ’yan siyasa cikin sabon yanayin rashin tabbas.
Kotun ta tabbatar da ingancin sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2), wadanda suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu.
Wasu daga cikin wadanda ake alakanta lamarin da su sun hada da tsohon IGP Mohammed Abubakar Adamu da Farfesa Isa Ali Pantami.
Asali: Legit.ng

