Maganganun da Tinubu Ya Gayawa Gwamna Adeleke bayan Sun Kebe a Villa
- Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Gwamna Ademola Adeleke na Osun da kada ya wulakanta abokan hamayyarsa bayan kammala zaben gwamna na jihar
- Tinubu ya ce Adeleke bai ci wani da yaki ba, sai dai ya lashe zabe, don haka ya kamata ya hada kan al’ummar Osun
- Shugaban kasar ya bukaci Adeleke ya tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da bin doka a lokacin mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja -Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun da kada ya kunyata ko wulakanta abokan hamayyarsa a zaben gwamna da aka kammala a jihar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026.

Source: Twitter
Mai girma Bola Tinubu ya ce Adeleke bai yi galaba a kan wani mutum ba, sai dai ya lashe zabe, cewar rahoton tashar Channels tv.
Me Tinubu ya gayawa Gwamna Adeleke?
“Kar ka kyamaci ko wulakanta wani daga cikin abokan hamayyarka,” ya fada wa gwamnan.
Ya ce al’ummar Jihar Osun sun bayyana matsayarsu ta hanyar zabar Adeleke saboda suna kaunarsa kuma suna son ya ci gaba da mulkarsu.
A cewar Tinubu, duk wanda ba ya murnar gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci bai cancanci farin ciki da jin dadin dimokuradiyya ba.
“Duk wani dan siyasa ko mai bin tsarin dimokuradiyya da ba zai iya murnar farin cikin zabe na gaskiya da adalci ba, bai cancanci dariya da farin cikin dimokuradiyya ba,” in ji shi.
Ya ja kunnen Gwamna Adeleke
Tinubu ya kuma gargadi Adeleke da kada ya tsangwami ko da mutum guda saboda nasarar da ya samu, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Kar ka tsangwami mutum saboda nasarar zabenka. Kar ka yi haka. Ba don kai kadai ba, ba don Osun kadai ba, har ma don al'umma masu zuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne ka gina hanyar hadin kai,”
“Kamar yadda na fada, ba ka ci wani mutum da yaki ba. Ka lashe zabe. Wannan shi ne abin da dimokuradiyya ta kunsa. Na yi matukar farin ciki da wannan tattaunawar da muka yi.” In ji shi.
Tinubu ya nemi a hada kan Osun
Shugaban kasar ya ce hanya mafi kyau da Adeleke zai nuna godiyarsa ga al’ummar Osun ita ce ya fadada akalarsa, ba ta hanyar yadda ya rera waka ko ya yi murnar nasarar ba, sai dai ta hanyar ayyukansa.
“Ka dauke ni a matsayin misali. Kuma ga inda na ke a yau. Allah ne Ya sanya ni a nan. Inda kake a yau, Allah ne Ya sanya ka a can. Ba saboda wayon wani daga cikin wadannan mutane ba,” in ji shi.

Source: Twitter
Ya kara da cewa goyon bayan mutane ne ya taimaka, ba wai wayonsu kadai ba. A cewar Tinubu, Adeleke yana cikin “matsayi na musamman” da zai ba shi damar kafa tarihi.
“Ka inganta hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali,” In ji shi.
Tinubu ya caccaki Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki alƙawarin Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027.
Tinubu ya ce irin wannan alƙawari ya nuna rashin fahimtar yadda harkokin gwamnati da tattalin arzikin Najeriya ke gudana, yana mai cewa cire tallafin ya taimaka wajen sauya yanayin kuɗin jihohi.
Asali: Legit.ng

