Dalibar BUK Ta Shiga Matsala da ta Taba 'Kimar' Hukumar EFCC

Dalibar BUK Ta Shiga Matsala da ta Taba 'Kimar' Hukumar EFCC

  • Dalibar Jami’ar Bayero, Kano, Maryam Isah Shehu, ta gurfana gaban kotun tarayya da ke Abuja kan zargin wallafa wani sako a kafar sada zumunta da ake cewa ya bata sunan EFCC
  • An gurfanar da Maryam Isah Shehu ne kan wani sakon Instagram da hukumar EFCC ta ce ya kunshi zargin cewa jami’anta sun lakada wa Ahmed Uthman duka bisa umarnin wani daraktan shiyya
  • Kotun ta dage sauraron bukatar belin dalibar zuwa 31 ga Agusta, bayan lauyanta ya ce ta shafe kusan kwanaki 30 a tsare kuma tana da jarabawa a ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Maryam Isah Shehu, dalibar shekarar karshe a Jami’ar Bayero, Kano (BUK), ta gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin wallafa wani sako a kafar sada zumunta da ake cewa ya bata sunan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).

Kara karanta wannan

An shiga fargaba da mace ta yi yunkurin kai harin bam a ginin majalisar Amurka

An gurfanar da Maryam Isah Shehu ne a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik kan tuhumar da EFCC ta gyara.

An gutfanar da dalibar BUK gaban kotu
Dalibar BUK, Maryan Isah Shehu da Ola Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Hukumar ta zarge ta da amfani da shafinta na Instagram, @maryam_shehu, wajen wallafa wani sako a ranar 21 ga watan Yunin, 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Abin da EFCC ta zargi dalibar

A cewar tuhumar da aka gyara, Halima Shehu ta wallafa wani sako da ke zargin cewa jami’an EFCC sun lakada wa wani Ahmed Uthman duka bisa umarnin wani daraktan shiyya wanda ake zargin ya karɓi N20m daga wani Usman Iya Abbas.

EFCC ta ce an wallafa sakon ne da nufin bata sunan hukumar. An tuhumi Shehu ne karkashin sashe na 24(2)(c) na dokar Cybercrimes (Prohibition, Prevention, Etc) Act ta 2015, wadda aka yi wa kwaskwarima a 2024. Hukumar ta ce laifin na karkashin sashe na 24(2)(c)(ii) na dokar.

Lauyan dalibar ya nemi belinta

A zaman kotun na ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026, lauyan Maryam Isah Shehu, Barrister Chiemela Ozioma Amalaha, ya nemi a saurari bukatar belin wadda yake karewa.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

Amalaha ya ce dalibar ta riga ta shafe kusan kwanaki 30 a tsare kafin a gurfanar da ita a gaban kotun.

Ya ce bangaren masu kare dalibar ya karɓi takardar tuhumar ne a safiyar Alhamis, sannan suka shigar da bukatar belin tare da mika kwafin ta ga masu gabatar da kara.

Sai dai masu gabatar da kara sun yi adawa da bukatar, suna cewa ba su samu isasshen lokaci ba na nazarin takardar neman belin.

Saboda haka, kotun ba ta saurari bukatar belin ba, inda ta dage shari’ar zuwa 31 ga Agusta, 2026, domin sauraron bukatar belin dalibar.

An tsare ta a Suleja

Kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Maryam Isah Shehu a a Gidan Gyaran Hali na Suleja har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.

Amalaha ya kuma sanar da kotun cewa dalibar na da jarabawar da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar.

Lauyan ya nemi kotun ta sa baki saboda tsawon lokacin da dalibar ta riga ta yi a tsare, musamman ganin cewa tana gab da rubuta jarabawarta.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

NANS ta shiga lamarin

Shugabannin kungiyar daliban Najeriya (NANS) sun tuntubi shugabannin EFCC domin neman hanyar warware matsalar da za ta kai ga janye shari’ar da ake yi wa Maryam Isah Shehu.

A wani sako a shafinta na X, kungiyar ta ce tana matukar damuwa da yadda lamarin ke iya shafar karatun dalibar da makomarta, musamman ganin cewa lokacin jarabawarta na gabatowa.

NANS ta ce tana tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa cikin tsari da lumana, tare da fatan samun mafita mai kyau.

EFCC ta gurfanar da dalibar BUK
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Tinubu ya ba EFCC umarni

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasarNajeriya, Bola Tinubu, ya ba Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC umarni game da kudaden da ake kwatowa.

Tinubu ya ba Hukumar EFCC umarni ta tura dukkan kudaden da aka kwace zuwa Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng