Maganganun da Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Peter Obi da Kwankwaso a Fadarsa

Maganganun da Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Peter Obi da Kwankwaso a Fadarsa

  • Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya buƙaci ’yan siyasa da magoya bayansu su guji zagi da kalaman rarrabuwar kawuna da ka iya haifar da tashin hankali
  • Peter Obi ya ce NDC na da niyyar gudanar da “siyasar kulawa da yi wa ’yan Najeriya hidima” tare da mai da hankali kan tsaro da ilimi
  • Obi ya yi kira ga ’yan Najeriya su zaɓi ’yan takarar NDC a 2027, tare da alkawarin amfani da albarkatun ƙasa wajen bunƙasa tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar ​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ’yan siyasa da su gudanar da harkokinsu cikin lumana, tare da guje wa kalaman da za su iya haifar da ƙiyayya da tashin hankali a tsakanin al’umma.

Sultan ya yi wannan kira ne ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026 lokacin da ya karɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, mataimakinsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na jam’iyyar, Dr Shamsu Haido.

Kara karanta wannan

Peter Obi da Kwankwaso sun ziyarci Sarkin Musulmi a Sokoto

Sarkin Musulmi ya gana da Kwankwaso da Peter Obi
Mai alfarma Sarkin Musulmi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa Sarkin Musulmin ya karbi bakuncinsu ne a fadarsa da ke Sokoto.

Sultan ya nemi a guji zagi da munanan kalamai

Sarkin Musulmin ya buƙaci ’yan siyasa da magoya bayansu su mutunta juna, su kare haɗin kan ƙasa, tare da guje wa zagi, cin mutunci da sauran abubuwan da ka iya jawo tashin hankali.

Ya ce ’yan siyasa suna da damar gabatar da manufofinsu da neman goyon bayan masu zaɓe, amma dole ne su gudanar da hakan bisa doka da kuma mutunta mutanen da suke da ra’ayoyin siyasa daban.

Muhammad Sa'ad Abubakar III ya jaddada cewa bai kamata a mayar da siyasa wata hanya ta raba kan al’umma ko haifar da ƙiyayya ba.

A cewarsa, muradun Najeriya da zaman lafiyar ƙasar ya kamata su kasance a gaba fiye da bambance-bambancen siyasa.

“Mukaman siyasa na wucin gadi ne”

Sarkin Musulmin ya ce mukaman siyasa na wucin gadi ne, yayin da zaman lafiya da haɗin kai suke da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan

"Ita ce hanya 1 tilo"; Na kusa da Atiku ya samo mafita ga 'yan adawa kan Tinubu . 2027

Ya kuma buƙaci shugabannin siyasa, musamman waɗanda ke neman mukaman gwamnati, su zama abin koyi ga sauran jama’a.

Hakazalika, ya ce ya kamata su tabbatar da cewa yakin neman zaɓensu bai zama sanadin rikici ko rarrabuwar kawuna a tsakanin jama’a ba.

Obi ya nemi a zaɓi ’yan takarar NDC

Da yake mayar da martani, Peter Obi ya gode wa Sarkin Musulmin bisa karɓar tawagar da kuma sauraron abubuwan da suka gabatar masa.

Obi ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da zaɓen 2027 wajen zaɓar ’yan takarar NDC a dukkan matakan gwamnati.

Ya ce wannan nauyi ne da ya rataya a kan kowa wajen tunkarar matsalolin da ƙasar ke fuskanta akai-akai.

Obi ya ce jam’iyyarsu ta himmatu wajen samar da abin da ya kira “siyasar kulawa da yi wa ’yan Najeriya hidima.”

Peter Obi ya ziyarci Sarkin Musulmi da tawagarsa
Muhammad Sa'ad Abubakar III tare da tawagar Peter Obi da Samata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Peter Obi ba zai sayi kuri'a ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi magana kan sayen kuri'u a zaben shekarar 2027.

Peter Obi ya ce takararsa ba za ta shiga harkar sayen ƙuri’u gabanin babban zaɓen 2027 ba da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng