Shirin Bola Tinubu na Tsaka Mai Wuya da APM Ta Aika Sako na Musamman Bankin Duniya

Shirin Bola Tinubu na Tsaka Mai Wuya da APM Ta Aika Sako na Musamman Bankin Duniya

  • APM ta bukaci Bankin Duniya da sauran masu ba da lamuni na kasa da kasa su dakatar da duk wata bukatar rance daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Jam’iyyar ta ce karin karbo bashi zai jinginar da makomar ’yan Najeriya, yayin da ake fama da tsananin matsin tattalin arziki
  • APM ta ce dan takararta, Seyi Makinde, zai mayar da hankali kan gaskiya, daidaita kashe kudade da farfado da bangaren samar da kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APM ya tunkari babban bankin duniya domin dakatar da yunkurin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na sake karbo bashi.

APM ta bukaci Bankin Duniya da sauran masu ba da lamuni na duniya su dakatar da duk wata sabuwra bukatar bashi da ta fito daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da sanarwa, ya hana bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A ruwayar jaridar Vanguarda, jam'iyyar adawan ta yi ikirarin cewa karin dauko wa kasa bashi zai jinginar da makomar ’yan Najeriya.

Kiran ya zo ne yayin da Najeriya shirin karbar rancen Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya, inda jam’iyyar ta nuna shakku kan yadda gwamnatin za ta iya biyan basussukan da ke kara yawa.

APM ta nuna damuwa kan ciyo bashi

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran APM na kasa, Abubakar Yusuf, ya fitar, APM ta ce gwamnatin Tinubu ba ta da cikakkiyar dabara ta biyan bashin da ya taru a karkashin mulkinta.

“APM ta yi kakkausar suka ga yunkurin Shugaba Tinubu na kara jinginar da makomar miliyoyin ’yan Najeriya ta hanyar sabon bashin dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya,” in ji Yusuf.

Jam’iyyar ta soki ci gaba da karbar bashi duk da karin kudaden shiga da aka samu bayan cire tallafin man fetur, tana mai cewa matakin ya zo ne a daidai lokacin da darajar Naira ke kara rauni.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Ta ce tun bayan da Tinubu ya hau mulki a 2023, ’yan Najeriya sun fuskanci karin haraji da hauhawar farashin abinci, wutar lantarki, sufuri, kiwon lafiya da sauran muhimman bukatun yau da kullum.

APM ta ambaci kiyasin Hukumar Abinci ta Duniya cewa kusan ’yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar matsananciyar yunwa a shekarar 2026, yayin da take zargin gwamnatin APC da yin ikirarin samun nasara duk da matsin da jama’a ke ciki.

APM ta nemi a hana Tinubu bashi

Jam’iyyar ta bukaci Bankin Duniya, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da sauran masu ba da lamuni ciki har da China da Amurka, da su ki amincewa da karin rance ga gwamnatin Najeriya, cewar rahoton Daily Trust.

Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da tambayin jam'iyyar adawa ta APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

APM ta ce dan takararta na shugaban kasa, Gwamna Seyi Makinde, zai mayar da hankali kan gaskiya, daidaita harkokin kasafin kudi, zuba jari mai inganci da farfado da bangaren samar da kayayyaki na Najeriya idan aka zabe shi.

Bashin da ake bin Najeriya zuwa 2025

Kun ji cewa alkaluma daga Hukumar Kula da Harkokin Bashi ta Kasa (DMO) sun nuna cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa karshen 2025.

Hakan na nufin idan aka raba wadannan kudade kan 'yan Najeriya, kowane mutum daya ana bin shi bashin kusan N724,000, a cewar wani bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262