Abin Tausayi: Jirgin Ruwa dauke da Mutane Sama da 70 Ya Kife a Sokoto

Abin Tausayi: Jirgin Ruwa dauke da Mutane Sama da 70 Ya Kife a Sokoto

  • Ana tunanin akalla mutum 40 sun rasa rayukansu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da manoma ya kife a Gorau, jihar Sokoto
  • Yawancin mutanen da ke cikin kwale-kwalen yara ne masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15 da haihuwa a duniya
  • An ceto mutum shida ciki har da dagacin ƙauyen, yayin da ake ci gaba da aikin neman waɗanda suka ɓace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Wani jirgin ruwa na kwale-kwale dauke da mutane da dama ya gamu da hatsari a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.

Ana tunanin akalla mutum 40 sun mutu bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da manoma zuwa gonakinsu na shinkafa ya kife a garin Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto.

Kwale-kwale ya kife a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne a lokacin da mutanen ke tsallaka wani rafi domin zuwa gonakinsu a kan kwale-kwalen da ke dauke da su.

Kara karanta wannan

Yadda walkiya ta fado kan mata mai ciki ta mutu har lahira a Bauchi

Jirgin ruwa ya kife da mutane a Sokoto

Rahotanni sun nuna cewa yawancin mutanen da ke cikin jirgin ruwan na kwale-kwalen yara ne kanana masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15 da haihuwa a duniya.

Wani ganau ba jiyau ya bayyana cewa akwai fiye da mutum 70 a cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife jim kaɗan bayan tashinsa.

An ce dagacin ƙauyen yana cikin mutanen da suka hau kwale-kwalen, amma an yi nasarar ceto shida ransa.

An gano gawarwaki da dama

Wani ɗan jarida na yankin, Sharhabilu Yahuza Kiliya, wanda yake wurin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa:

"Ya zuwa yanzu, mun gano gawarwaki kusan 40, yayin da aka ceto mutum shida, ciki har da shugaban ƙauyen."

A cewarsa, mutanen da lamarin ya rutsa da su sun haɗa da masu gonaki da ma’aikatan da aka ɗauka domin aikin girbin shinkafa.

Sharhabilu Yauza Kikiya ya kuma kara da cewa kwale-kwalen da ke dauke da mutanen masu yawa ya kife ne a cikin rafin jim kaɗan bayan tashinsa.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da 'yan yawon bude ido ya rikito, rayuka sun salwanta

“Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, inda masu fito na yankin ke neman mutanen da suka ɓace tare da fitar da gawarwaki,” in ji shi.
Jirgin ruwa ya kife a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto Hoto: Dr. Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Lamarin dai na zuwa ne bayan an samu irin wannan hatsarin na jirgin ruwa a jihar Neja, wanda ya ritsa da manoma da ke kan hanyar zuwa gonakinsu

Hatsarin wanda ya auku a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyar da suka hada da maza hudu da mata biyar, bayan jirgin ruwan ya nutse.

Jirgin sama ya rikito daga sararin samaniya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu da ke dauke da masu yawon bude ido ya yi hatsari a Dutsen Ololokwe da ke gundumar Samburu a tsakiyar Kenya.

Jami'an hukumar kula da hadurran jiragen sama sun tabbatar da cewa dukkanin mutane shida da ke cikinsa suka rasa rayukansu.

Hukumar KCAA ta ce jirgin na kan wani yawon shakatawa ta sama ne daga wani wurin kiwon namun daji a Losaiba zuwa Ewaso Nyiro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng