'Yan Sanda Cafke Kwamishina da Wasu Mutane 4 kan Kashe Darakta

'Yan Sanda Cafke Kwamishina da Wasu Mutane 4 kan Kashe Darakta

  • ’Yan sanda a Delta sun kama Kwamishinan Ilimin Sakandare, Dr. Kingsley Ashibogwu, da wasu mutane huɗu yayin binciken mutuwar Unity Adeda
  • Rundunar ta ƙaddamar da farautar wasu mutane biyu da ta ce ana buƙatar su domin taimaka wa binciken da ake gudanarwa kan lamarin
  • ’Yan sanda sun ce za su gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci, kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukuncin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Delta - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta kama Kwamishinan Ilimin Sakandare na jihar, Dr. Kingsley Ashibogwu, da wasu mutane huɗu kan mutuwar Unity Ekpevbughe Adeda, mataimakin darakta a ma’aikatar.

Rundunar ta kuma ce ta ƙaddamar da farautar wasu mutane biyu da ta bayyana a matsayin waɗanda ake ganin suna da muhimmiyar alaƙa da binciken mutuwar Adeda.

'Yan sanda sun cafke kwamishina a Delta
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Delta, SP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An kama matasa 2 kan kashe uwa mai 'ya'ya 5 yayin satar waya a Gombe

An tsare mutane biyar

A cewar sanarwar, kamen kwamishinan da sauran waɗanda ake zargi wani ɓangare ne na binciken da rundunar ke gudanarwa domin gano abin da ya faru da Unity Adeda.

Rundunar ta ce hakan ya sa adadin mutanen da take tsare da su dangane da binciken ya kai mutum biyar.

An fara neman wasu mutane biyu

Rundunar ta kuma sanar da ƙaddamar da farautar Mrs Clemetine Ufuoma, Daraktar Ilimin Firamare da Sakandare, da Clement Apia, direban Kwamishinan Ilimin Sakandare.

’Yan sandan sun ce ana buƙatar mutanen biyu domin taimaka wa ci gaba da binciken lamarin.

Rundunar ta yi kira ga mutanen biyu da su gaggauta gabatar da kansu ga jami’an bincike ba tare da ƙarin ɓata lokaci ba.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Delta, Samuel E. Erale, ya kuma yi kira ga waɗanda ake nema, a duk inda suke, da su kasance a shirye su gabatar da kansu ga rundunar.

Kara karanta wannan

An fara: Matasa sun yayyaga hotunan tallar Tinubu a Arewacin Najeriya

’Yan sanda sun yi alƙawarin yin cikakken bincike

A cewar sanarwar, kwamishinan ’yan sandan ya sake jaddada cewa za a gudanar da binciken lamarin cikin cikakken tsari, ba tare da nuna son kai ba, kuma cikin ƙwarewa.

Ya ce duk wanda aka tabbatar da cewa yana da hannu a mutuwar Adeda zai fuskanci hukuncin doka, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Rundunar ta kuma tabbatar wa iyalan marigayin da sauran jama’a cewa za a bi dukkan matakan doka wajen gano ainihin abubuwan da suka haifar da mutuwar mataimakin daraktan.

An kama kwamishina a Delta
Taswirar jihar Delta, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun cafke mai satar yara

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan sanda a Edo sun kama wani mai ikirarin malamin addini ne kuma mai kula da Divine Grace Church, Nicholas Nusa, mai shekaru 50, bisa zargin sace yara mata biyar a jihar.

Nicholas Nusa, wanda ke gudanar da cocin a kan titin Imoga da ke Ibillo, karamar hukumar Akoko-Edo, ana kuma zarginsa da yi wa daya daga cikin yaran, mai shekaru 15, ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng