"Ku Daina Jira": Ministan Tinubu Ya ba Matasan Najeriya Shawara kan Gwamnati
- Ministan Matasa Ayodele Olawande ya bukaci matasan Najeriya su daina jiran taimakon gwamnati ko yanayi mai kyau, su yi amfani da damar da ke akwai domin gina makomarsu
- Olawande ya ce matasa ne babbar kadara ta Najeriya, yayin da gwamnati ta samar da shirye-shiryen koyar da sana’o’i, jari da samar da ayyukan yi
- Ministan ya bayyana cewa matasa miliyan bakwai sun samu horo, yayin da aka samar da ayyukan yi miliyan biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Matasa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Ayodele Olawande, ya bayar da shawara ga matasa kan jiran gwamnati.
Olawande ya bukaci matasan Najeriya su daina jiran samun alaka da gwamnati ko cikakken yanayi kafin su fara gina makomarsu, inda ya ce lokaci ya yi da za su yi amfani da damar da ke gabansu.

Kara karanta wannan
Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Source: Twitter
Olawande ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026 a Abuja, yayin kaddamar da littafin No More Future: Why Waiting Is Over, What to Build Instead, wanda Christopher Olusa ya rubuta, cewar rahoton Daily Trust.
Ministan, wanda Dotun Omoleye ya wakilta, ya ce babbar kadara da Najeriya ke da ita ba albarkatun kasa ba ne, sai dai matasanta.
Lokacin jira ya wuce
"Lokacin jiran gwamnati ta gyara komai kafin a fara neman mafita, jiran samun alaka mai kyau kafin a fara aiki, da jiran izini domin zama abin da muke da damar zama, ya wuce.” In ji shi.
Olawande ya ce gwamnati, karkashin ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu, ta bullo da shirye-shiryen da ke bai wa matasa dabaru, jari da damammaki.
Ya bayyana cewa an horas da matasan Najeriya miliyan bakwai, yayin da aka samar da ayyukan yi miliyan biyar.
Ya kara da cewa matasa 239,726 sun samu horo kan dabarun zamani da na aiki ta hannun Nigerian Youth Academy (NiYA).
A cewarsa, an kuma bayar da takardun shaidar kammala horo sama da miliyan 1.2 ga matasan da suka samu horon.
Gwamnati ta tallafa wa matasa
“Ta hanyar NiYA StartUp, an bai wa matasa ’yan kasuwa 200 Naira miliyan daya kowannensu, yayin da wasu ’yan Najeriya 200 da ke sana’o’in hannu suka samu tallafin Naira 500,000 kowannensu,” in ji shi.
Ministan ya ce gwamnati na kuma sake fasalin shirin National Youth Service Corps (NYSC), domin mayar da shi daga shirin da ake gudanarwa kawai zuwa wani dandali na koyon sana’a, kasuwanci da gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma.
Shi ma shugaban kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da NELFUND, Ifeoluwa Ehindero (APC, Ondo), ya ce littafin ya kalubalanci tunanin jiran gwamnati, aiki ko wata dama.
“Makoma ba wani abu ba ce da ya kamata mu jira kawai; abu ne da dole mu himmatu wajen samarwa,” in ji shi.

Source: Twitter
Atiku ya ba matasa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi muhimmin kira ga matasa.
Atiku ya bukaci matasan Najeriya su daina tsaya wa kan yin korafi game da rashin kyakkyawan shugabanci, su shirya karɓar ragamar shugabanci gabanin babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

