Sanatan da Ya Fice daga APC Ya Samu Tikitin PDP, Zai Fafata da Gwamna a 2027

Sanatan da Ya Fice daga APC Ya Samu Tikitin PDP, Zai Fafata da Gwamna a 2027

  • Sanata Saliu Mustapha mai wakiltar Kwara ta Tsakiya ya karɓi tikitin PDP domin sake neman kujerarsa a zaɓen 2027
  • Mustapha ya sauya sheka zuwa PDP ne sa’o’i kaɗan bayan ya sanar da ficewarsa daga APC sakamakon doguwar rashin jituwa da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq
  • Sauya shekarsa ya kafa babban fafatawa a Kwara ta Tsakiya tsakanin shi da gwamnan da ya samu tikitin APC na wannan mazabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Ilorin, jihar Kwara - Rikicin siyasa da ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kwara ya ɗauki sabon salo, yayin da Sanata Saliu Mustapha mai wakiltar Kwara ta Tsakiya ya karɓi tikitin PDP domin neman kujerar sanata a zaɓen 2027.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan sanatan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar mai mulki sakamakon doguwar rashin jituwa tsakaninsa da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Kara karanta wannan

INEC ta yi maganar goyon bayan wani dan takara ko jam'iyya a zaben 2027

Saliu Mustapha ya koma jam'iyyar PDP
Sanata Saliu Mustapha tare da shugaban PDP wajen karbar fom Hoto: Senator Saliu Mustapha
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Juma’a, 21 ga watan Agustan 2026 ne Mustapha ya karɓi fom ɗin tsayawa takarar sanata na PDP a hukumance, inda shugaban PDP na Jihar Kwara, Hon. Isa Adamu Baw, ya miƙa masa fom ɗin.

Jami’an jam’iyyar sun bayyana cewa an bai wa Mustapha tikitin ne bayan tattaunawa da tsohon ɗan majalisa Moshood Mustapha, wanda a baya ake tunanin zai samu tikitin PDP na kujerar sanata ta Kwara ta Tsakiya.

Babban fafatawa a Kwara ta Tsakiya a 2027

Sauya shekar Mustapha zuwa PDP ya kafa wani babban fafatawa a siyasar Kwara ta Tsakiya, inda ake sa ran sanatan zai kara da gwamnan, wanda ya riga ya samu tikitin APC na wannan mazabar.

Ficewar Mustapha daga APC ta biyo bayan watanni na rashin jituwa a cikin jam’iyyar, musamman bayan zaɓen fidda gwani na takarar gwamna, wanda Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi Salihu, ya lashe.

Kara karanta wannan

Takarar Obi da Kwankwaso ta gamu da cikas, rikicin shugabanci ya raunana ta

Mustapha na cikin manyan masu neman takara da masu ruwa da tsaki da suka ƙi amincewa da wasu ɓangarorin tsarin zaɓen, sannan ya kasance cikin ɓangaren G15 na masu ƙorafi.

A cikin sanarwar da ya fitar kan ficewarsa, Mustapha ya ce ya yanke shawarar ne bayan shafe makonni yana tuntubar masu ruwa da tsaki, magoya bayansa da kuma al’ummar da yake wakilta.

PDP ta shirya karɓar Mustapha

Komawar Mustapha PDP ta tabbatar da jita-jitar da ta shafe makonni ana yi cewa jam’iyyar adawar na shirin karɓar sa a Kwara ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna a baya cewa PDP na duba yiwuwar ba shi tikitin takarar sanata bayan rikicinsa da APC, yayin da aka ce tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyun adawa suna ƙoƙarin jan hankalinsa.

Shigar Mustapha PDP ya mayar da rikicin cikin gida na APC zuwa babban fafatawar zaɓen 2027, inda sanatan mai ci zai koma jam’iyyar adawa domin kare kujerarsa daga hannun gwamnan.

Wannan sauyi na iya kuma haifar da ƙarin sauye-sauyen siyasa tsakanin mambobin ɓangaren APC masu ƙorafi gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi wa APC yasa a Kano, manya a jam'iyyar sun rungumi Kwankwasiyya

Saliu Mustapha ya samu tikitin PDP
Sanata Saliu Mustapha mai wakiltar Kwara ta Tsakiya Hoto: Senator Saliu Mustapha
Source: Facebook

Gwamnan Kwara ya raba motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya miƙa motoci hudu ga Babban Limamin Ilorin da wasu manyan malaman addini a masarautar Ilorin.

An gudanar da bikin miƙa motocin ne a fadar Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, inda manyan jami'an gwamnati da shugabannin addini suka halarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng