Akwai Matsala: Birtaniya Ta Gargadi Masu Shirin Zuwa Gombe, Katsina da Wasu Jihohi 9 a Najeriya

Akwai Matsala: Birtaniya Ta Gargadi Masu Shirin Zuwa Gombe, Katsina da Wasu Jihohi 9 a Najeriya

  • Kasar Birtaniya ta hana ’yan kasarta zuwa wasu sassan jihohin Najeriya 11 saboda matsalar tsaro da ta kara kamari
  • Ta kuma jero wasu jihohi 19 da Abuja da ta sanya ƙarƙashin shawarar yin tafiya idan ya zama dole
  • Ofishin FCDO ya bayyana wa yan Birtaniya cewa babu tabbacin kowace tafiya zuwa wadannan jihohi za ta kasance cikin aminci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Birtaniya ta shawarci ’yan kasarta da kada su yi tafiya zuwa wasu sassan jihohin Najeriya 11 saboda matsalolin tsaro.

Haka zalika Birtaniya ta sanya wasu jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, ƙarƙashin shawarar yin tafiya idan ya zama dole.

Birtaniya.
Firaministan kasar Birtaniya, Andy Burnham yana jawabi ga ma'aikata lokacin da ya kai ziyara ofishin kula da dumamar yanayi a Exeter Hoto: Finnbarr Webster
Source: Getty Images

Leadership ta ce shawarar tana kunshe cikin sabuwar sanarwar tafiye-tafiye zuwa Najeriya da Ofishin Harkokin Waje, da Ci Gaban Birtaniya (FCDO) ya fitar ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba Ahmad ya fadi abin da zai sa Tinubu ya fadi zabe kafin karfe 4:00

Jihohin da aka hana yan Birtaniya zuwa

A cewar sanarwar, gwamnatin Birtaniya ta shawarci ’yan kasarta da kada su yi tafiya zuwa Borno, Yobe, Adamawa da Gombe a yankin Arewa maso Gabas.

Katsina da Zamfara a Arewa maso Yamma ma na cikin jihohin da Birtaniya ta hana ’yan kasarta zuwa.

A yankin Kudu maso Kudu kuma, shawarar ta shafi yankunan rafuka na Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River.

FCDO ta bayyana yankunan rafukan da abin ya shafa a matsayin “wuraren koguna da fadama da ake iya isa gare su ta jirgin ruwa, amma ba ta hanya ba.”

Jihohin da ke ƙarƙashin wannan shawarar sun haɗa da:

  1. Borno
  2. Yobe
  3. Adamawa
  4. Gombe
  5. Katsina
  6. Zamfara
  7. Yankunan rafuka na Delta
  8. Yankunan rafuka na Bayelsa
  9. Yankunan rafuka na Rivers
  10. Yankunan rafuka na Akwa Ibom
  11. Yankunan rafuka na Cross River

Jihohin da ake bukatar kulawa

FCDO ta kuma shawarci ’yan kasarta da kada su yi tafiya zuwa Bauchi, Abuja da wasu jihohi 16 sai di idan abin da za su yi ya zama dole.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Wuraren da ke ƙarƙashin shawarar “yin tafiya idan ya zama dole” sun haɗa da:

  1. Bauchi
  2. Kaduna
  3. Kano
  4. Kebbi
  5. Jigawa
  6. Sokoto
  7. Niger
  8. Kogi
  9. Plateau
  10. Taraba
  11. Kwara
  12. Benue
  13. Abia
  14. Anambra
  15. Imo
  16. Yankunan Delta da ba na rafuka ba
  17. Yankunan Bayelsa da ba na rafuka ba
  18. Yankunan Rivers da ba na rafuka ba
  19. Babban Birnin Tarayya, Abuja
Jirgin sama.
Jirgin sama yayin da yake tsakiyar tafiya a sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Birtaniya ta gargadi matafiya

FCDO ta gargadi matafiya cewa “babu wata tafiya da za a iya tabbatar da cewa za ta kasance cikin aminci”, tare da kira ga ’yan Birtaniya da ke shirin zuwa Najeriya da su duba shawarwarin tafiye-tafiye.

Ta kuma shawarci matafiya da su binciki wuraren da suke shirin ziyarta tare da samun inshorar tafiya da ta dace kafin tafiya, kamar yadd Vanguard ta kawo.

Gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin cewa inshorar tafiya na iya zama ba shi da inganci idan mutum ya yi tafiya saɓanin shawarar FCDO.

Birtaniya na neman masu wasu kadarori

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Birtaniya ta fitar da jerin kadarorin marayu da har yanzu ba a karɓa ba, ciki har da kadarori 60 da ke da alaƙa da 'yan Najeriya.

Daga cikin wadannan mutane 60, an ce maza ne suka fi yawa a cikinsu, kuma jihar Legas ce jihar da suka fi fitowa daga cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262