An kai Dangote Kotun Kenya, an Kawo Masa Cikas wajen Gina Matatar Mai

An kai Dangote Kotun Kenya, an Kawo Masa Cikas wajen Gina Matatar Mai

  • Wata kotu a Kenya ta umarci a dakatar da wasu ayyukan da suka shafi wurin da ake shirin gina matatar mai ta Dangote da ta kai darajar $16bn
  • Matakin kotun ya biyo bayan ƙarar da wasu mazauna Lamu suka shigar, inda suka yi zargin cewa aikin zai tauye haƙƙoƙinsu kan filayensu
  • Sai dai Dangote ya ce umarnin kotun ba ya hana gudanar da bikin aza harsashin ginin matatar da aka shirya yi ranar Laraba mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wata kotu a Kenya ta bayar da umarnin a ci gaba da kiyaye yadda filin da ake shirin gina matatar mai ta Dangote yake a halin yanzu, har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar a ranar 14 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan

Malaman da aka sace a hanyar zuwa yi wa Tinubu addu'a sun shafe mako 2 a daji

Matatar da ake shirin ginawa a Lamu, Arewa maso gabashin Kenya, na da darajar kusan $16bn kuma ana sa ran za ta taimaka wajen rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga wasu ƙasashe.

Alhaji Aliko Dangote
Aliko Dangote na maga a wajen taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mazauna Lamu sun kai ƙara

Jaridar Bloomberg ta ruwaito cewa Mai Shari’a Jane Onyango ce ta bayar da umarnin a kiyaye yadda lamarin yake a filin da ake takaddama a kai.

An bayyana cewa mutane 133 da suka bayyana kansu a matsayin manoma da mazauna Lamu ne suka shigar da ƙarar, suna zargin cewa aikin zai tauye haƙƙinsu kan filayensu.

Bugu da kari, masu ƙarar sun kuma yi zargin cewa za a tilasta korarsu daga filayensu tare da lalata kadarorinsu, ba tare da samar musu da tsarin sake tsugunar da su ba.

Zargin karya dokokin muhalli

Masu ƙarar sun kuma zargi Dangote da hukumomin Kenya da rashin bin dokokin muhalli na ƙasar, waɗanda suka tanadi gudanar da cikakken binciken tasirin muhalli kafin fara manyan ayyuka.

A cewar takardun ƙarar da aka bayyana, mutanen sun kuma yi zargin cewa aikin bai cika wasu sharudan kundin tsarin mulkin Kenya ba, musamman batun gudanar da shawarwari tare da jama’ar da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Matar aure ta kashe kishiyarta a yanayi mara daɗin ji, an gano cutar da ke damunta

Rahoton the Cable ya nuna cewa kotun ta tsara ranar 14 ga Oktoba domin ci gaba da sauraron batun, yayin da ta umarci ɓangarorin da su kiyaye halin da filin yake ciki zuwa wannan lokaci.

Matatar Dangote
Matatar Aliko Dangote da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Batun shiga harkar lantarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Aliko Dangote ya bayyana shirin zuba sama da $10bn a fannin samar da wutar lantarki a Afirka, matakin da ka iya sauya yadda ake rabon jarinsa tsakanin wasu tsare-tsaren kasuwanci.

Nahiyar Afirka na fuskantar babban gibin samun wutar lantarki, inda bayanan shekarar 2024 suka nuna cewa kusan mutane miliyan 600 a yankin Afirka da ke kudu da Sahara ba su da wutar lantarki.

Masana sun ce kamfanonin masana’antu na Dangote na iya zama masu amfani da wutar da ayyukan za su samar, abin da zai iya rage wasu daga cikin haɗuran da ake tsoron faruwarsu idan kamfanin ya fara aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng