Amurka Ta Sake Taimaka wa Najeriya, An Gano Wani Sinadari Mai Matukar Hadari a cikin Daji
- Hukumar NDLEA ta Najeriya ta yi nasarar gano wani sinadari da ake amfani da shi wajen samar da allurar fenta mai matukar hadari
- Shugaban NDLEA, Buba Marwa ya ce kayan aikin binciken sinadarai da Amurka ta samar sun taimaka wajen gano sinadarin
- Rahoto ya nuna cewa an gano sinadarin ne a wani katafaren dakin binciken methamphetamine a dajin jihar Ogun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Buba Marwa, ya ce sun gano wani sinadari da ake amfani da shi wajen hada allurar fenta mai matukar hadari.
Marwa ya ce kayan aikin binciken sinadarai da Amurka ta samar sun taimaka wa NDLEA wajen gano wani sinadari da ake alakanta shi da samar da fenta, wacce masu ta'amali da miyagun kwayoyi ke amfani da ita.

Source: Facebook
NDLEA ta gano sinadari a dajin Ogun
A rahoton The Cable, shugaban na NDLEA ya ce an gano sinadarin ne a wani dakin binciken methamphetamine da aka gano a wani daji a jihar Ogun.
Marwa ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da Derek Tolliver, Daraktan Ofishin Harkokin Miyagun Kwayoyi na Amurka (INL) a Najeriya, ya jagoranci tawaga zuwa hedikwatar NDLEA da ke Abuja.
A watan Mayu ne NDLEA ta tarwatsa wani ɓoyayyen dakin binciken a wani daji a Ogun, inda aka gano kayayyaki da sinadarai da darajarsu ta haura Naira biliyan 480.
An kama mutane bakwai a samamen, ciki har da ’yan Najeriya huɗu da ’yan kasar Mexico uku.
An gano sinadarin haɗa fenta
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce Marwa ya bayyana cewa kayan aikin binciken sinadarai da INL ta samar sun taimaka wa hukumar wajen gano sinadarin yayin da ake nazarin abubuwan da aka kwato daga dakin binciken.
Ya ce da ba a samu kayan aikin zamani na binciken sinadarai ba, da ba a gano sinadarin ba, saboda ƙaramin kaso ne kawai yake cikin sauran sinadaran da aka kwato.
Fenta na da wani ƙarfi mai tsananin tasiri a cikin magungunan opioid na roba, wanda ake amfani da shi wajen rage radadi da kuma sanya marasa lafiya cikin yanayin barci yayin wasu ayyukan jinya.
Sai dai yawan amfani da shi fiye da kima na iya haifar da matsaloli masu tsanani, ciki har da suma, gazawar numfashi da mutuwa.

Source: Facebook
NDLEA ta tuna gargadi da ta yi
A shekarar 2022, NDLEA ta gargadi jama'a kan shirin da wasu “ƙungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi” ke yi na shigar da fentanyl mai haɗari cikin kasuwar Najeriya.
Marwa ya ce gano sinadarin da ake amfani da shi wajen samar da fentanyl ya zama babban abin damuwa.
“Mun gano cewa ɗaya daga cikin sinadaran farko a zahiri ana amfani da shi wajen samar da fentanyl, wanda ba labari mai daɗi ba ne. Babu wanda yake son jin wannan kalmar,” in ji Marwa.
NDLEA ta rusa ramuka a Kano
A wani labarin, kun ji cewa jami’an hukumar NDLEA sun gano tare da rusa ramuka da kogo da ake amfani da su wajen fataucin miyagun ƙwayoyi da ajiyarsu a Kano.
NDELA ta bayyana cewa hakan na cikin kokarin ta na farautar masu safara da sayar da miyagun kwayoyi a Kano da Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng

