Gargadin da Janar Babangida Ya Yi Wa Obasanjo kan Atiku
- Donald Duke, tsohon gwamnan Cross River, ya bayyana yadda Ibrahim Babangida ya gargadi Olusegun Obasanjo kan Atiku Abubakar
- Duke ya ce rikicin Obasanjo da Atiku ya tsananta yayin da tsohon shugaban kasar ke shirin neman wa’adi na biyu
- Olusegun Obasanjo dai da Atiku Abubakar sun yi aiki tare a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 a matsayin shugaban kasa da mataimaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Donald Duke, tsohon gwamnan Cross River, ya bayyana yadda Ibrahim Babangida ya gargadi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan mataimakinsa Atiku Abubakar.
Donald Duke ya kasance gwamnan jihar Cross River da ke yankin Kudu maso Kudu daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce ya bayyana labarin ne a cikin sabon littafin Seun Oloketuyi mai suna How to Win Elections in Nigeria, wanda ya yi bayani kan dabarun siyasar farkon jamhuriya ta hudu a Najeriya.
Taron shugabannin Najeriya
Duke ya ba da labarin yadda wani taro na wasu tsofaffin shugabannin Najeriya da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ya rikide zuwa wani yanayi mai cike da tashin hankali.
Taron ya samu halartar Babangida, Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa, Obasanjo da Atiku.
Duke ya ce taron ya zo da wani gargadi kai tsaye da ba za a manta da shi ba daga Babangida, wanda ya sauya yanayin alakar siyasar Obasanjo da Atiku.
A cewar Duke, alakar da ke tsakanin Obasanjo da Atiku ta fara tabarbarewa yayin da shugaban kasar ke shirin neman wa’adi na biyu.
Ya ce Atiku na daukar wasu matakai da suka jawo damuwa kan ko zai ci gaba da mara wa Obasanjo baya a kokarinsa na sake lashe zabe.
An samu rashin jituwa
Littafin ya bayyana cewa karuwar rashin jituwar ta zama babbar matsala ta siyasa a cikin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Duke ya tuna cewa a wani lokaci, gwamnoni 10, ciki har da shi, sun gana da Solomon Lar, shugaban PDP na kasa a lokacin, domin tattauna yiwuwar sauya wanda zai rike mukamin mataimakin shugaban kasa. Ya ce lamarin ya yi matukar damun Obasanjo.
Duke ya ce ya tuna yadda shugaban kasar ya kira shi da daddare yana korafin abin da ya kira cin amanar da mataimakinsa ya yi masa.
“Na roke shi da ya kwantar da hankalinsa, sannan na yi masa alkawarin zan tashi zuwa Abuja da safe,” in ji Duke.
Abin da ya biyo baya shi ne wani taro na daban a fadar shugaban kasa. A cewar Duke, Atiku ne ya shirya ganawar Babangida da Abdulsalami da Obasanjo.
“Na gargade ka kan mataimakinka”
A yayin taron, an ce Babangida ya tunasar da Obasanjo kan yarjejeniyoyin da aka cimma bayan an sake shi daga gidan yari.
Ya kuma yi ikirarin cewa zai kasance da wahala a shawo kan shugabannin siyasar Arewa su mara wa Obasanjo baya domin ya sake samun wa’adi na biyu.
Duke ya ce Obasanjo ya tambaye su ko wannan shi ne matsayinsu na karshe ko kuma har yanzu akwai damar yin sulhu. An ce Babangida ya amsa cewa har yanzu akwai damar ci gaba da tattaunawa.

Kara karanta wannan
Miyagun kwayoyi: Dubun tsohon shugaban ƙaramar hukuma ta cika, ya shiga hannu a Kano
Sai dai a cewar Duke, abin da ya fi daukar hankali ya faru ne bayan da taron ya kusa karewa. Ya ce yayin da mutanen ke fita daga dakin Obasanjo na kashin kansa, Babangida ya ce ya manta makullansa a ciki, sannan ya nemi Obasanjo ya koma tare da shi.
Me Babangida ya gayawa Atiku?
Yayin da mutanen biyu suka koma su kadai, an ce Babangida ya sauke salon diflomasiyyarsa ya yi wa Obasanjo gargadi kai tsaye.
“Na gargade ka kada ka yarda da wannan mataimakin na ka,” in ji shi ga Obasanjo.
Lokacin da suka koma wajen sauran mutanen, Babangida ya kalli Atiku kafin ya juya ya dubi Obasanjo.
“Wannan ba zai iya mulkin Najeriya ba,” in ji shi, a cewar Duke.
Duke ya ce ganawar ta ba da haske kan yadda rashin amincewa tsakanin Obasanjo da Atiku ya yi zurfi, da kuma irin muhimmancin da aka bai wa takaddamar siyasar tasu a bayan fage.
Ya kara da cewa lamarin ya kara tabbatar masa da daya daga cikin darussan da ya koya a lokacin da yake kan mulki, wato, “cin amana abu ne mai matukar hauka a siyasa”.

Source: Facebook
Atiku ya yi wa Obasanjo gori
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya ce ya ciyar da Olusegun Obasanjo tare da tufatar da shi bayan ya fito daga gidan yari.
Atiku ya ce a lokacin da Obasanjo ya samu ’yanci, ba shi da wani abu mai yawa, don haka ya karbe shi tare da tabbatar da cewa an kula da shi yadda ya kamata kuma bai rasa komai ba.
Asali: Legit.ng

