"Ina da Tabbaci": Jigo a APC Ya Fadi Yankin da Tinubu Zai Lashe a 2027

"Ina da Tabbaci": Jigo a APC Ya Fadi Yankin da Tinubu Zai Lashe a 2027

  • Olusola Adeyeye ya ce APC za ta yi aiki tuƙuru domin samun nasara, yana mai cewa jam’iyyar za ta lashe muhimmin yanki da gagarumin rinjaye
  • Adeyeye ya ce duk jam’iyyar da ta shiga zaɓe ba tare da haɗin kai ba na iya fuskantar rashin nasara a zaɓen 2027
  • Tsohon sanatan ya ce Rauf Aregbesola ba zai iya mayar da farin jinin da yake da shi ga wani ɗan takara ba, matuƙar ba shi ne ɗan takarar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 16 ga Janairu, 2027, tsohon ɗan majalisar dattWa mai wakiltar Osun ta Tsakiya, Olusola Adeyeye, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a Kudu maso Yamma.

Adeyeye, wanda shi ne jagoran kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na APC a Kudu maso Yamma, ya ce duk wanda yake ganin zaɓen 2027 zai kasance mai sauƙi yana yaudarar kansa.

Kara karanta wannan

"Yanzu ne lokacin": Atiku ya sake aika sako ga 'yan Najeriya kan Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu na neman tazarce a 2027
Mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanata Adeyeye ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Tv.

Adeyeye ya ce APC za ta yi gagarumae nasara

Tsohon sanatan ya bayyana cewa duk wata jam’iyya da ta shiga zaɓe ba tare da haɗin kai tsakanin ‘ya’yanta ba, tana iya fuskantar matsalar rashin nasara.

Sai dai Adeyeye ya ce a halin da siyasar Najeriya take ciki, bai ga wata jam’iyya da za ta iya kayar da APC a duk inda jam’iyyar mai mulki ta samu haɗin kai a Kudu maso Yamma ba.

Ya ce APC na aiki tuƙuru domin ganin ta samu nasara, yana mai cewa jam’iyyar za ta yi gagarumar nasara.

“Na faɗa a fili cewa duk wanda yake ganin zaɓe na gaba zai kasance mai sauƙi ga jam’iyyarsa, yana yaudarar kansa. Mu a APC muna aiki tuƙuru domin samun nasara, kuma ina tabbatar muku cewa za mu yi nasara,” in ji shi.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa APC na da burin samun nasara a dukkan jihohin Kudu maso Yamma.

“Ina kuma tabbatar muku cewa za mu yi babbar nasara. Ina son mu lashe Kudu maso Yamma, kuma za mu ba kowa mamaki,” in ji shi.

Ya kawo misalin Obasanjo

Adeyeye ya ce ko da Shugaba Tinubu ya rasa kuri’un Kudu maso Yamma, hakan ba lallai ya hana shi zama shugaban ƙasa ba.

Sai dai ya jaddada cewa bai yi imanin Tinubu zai rasa yankin ba, yana tunatar da yadda tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya taɓa samun ƙarancin kuri’u a yankinsa amma daga baya ya zama shugaban Najeriya.

“A mafi munin yanayi, mu ce Bola Tinubu ya rasa Kudu maso Yamma, duk da cewa na tabbatar muku ba zai faru ba. Shin mun manta cewa wani Bayerabe ya rasa Kudu maso Yamma amma ya zama shugaban ƙasa?” ya tambaya

Ya ƙara da cewa Obasanjo ya rasa gundumarsa, rumfar zaɓensa, jiharsa da ma wasu jihohin Kudu maso Yamma, amma duk da haka ya samu damar zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare

An yi hasashen nasarar Shugaba Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

APM ta bukaci Tinubu ya hakura da takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APM ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Jam'iyyar APM ta kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya mara wa dan takararta na shugaban kasa, Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng