Kurunkus: Atiku Ya Fadi Lokaci na Karshe da Zai Yi Takarar Shugabancin Najeriya
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi magana kan lokacin da zai daina neman shugabancin Najeriya
- Atiku Abubakar wanda ya sha yin takarar shugaban kasa ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026
- Ya kuma bukaci masu katin zabe su fito su kada kuri’a tare da zama a rumfunan zabe domin tabbatar da an kirga kuri’unsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana lokacin da zai daina neman kujerar shugaban kasa.
Atiku Abubakar ya ce ba zai sake neman takarar shugaban kasar Najeriya ba idan ya sha kaye a zaben 2027.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026 wadda ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa
Yaushe Atiku zai daina takara?
Lokacin da aka tambaye shi ko zai sake neman shugabancin kasar idan bai yi nasara a zaben 2027 ba, sai tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:
“A’a, na taba fada a baya, tun daga wannan zaben, ba zan sake takara ba.”
Atiku, wanda ya taba neman shugabancin Najeriya sau da dama, ya kuma bukaci ’yan Najeriya masu katin zabe na dindindin (PVC) da su fito su kada kuri’a a zaben 2027.
Ya jaddada muhimmancin masu kada kuri’a su ci gaba da zama a rumfunan zabe domin tabbatar da an kirga kuri’unsu.
Atiku ya bukaci masu kada kuri'a su fito
Atiku ya ce masu katin zabe su fito domin kare makomarsu, ta iyalansu da kuma makomar kasar.
“Da farko, ina rokon wadanda suke da katin zabe, saboda kansu, iyalansu da makomarsu, su fito su kada kuri’a. Wannan ita ce mafita ga matsalolin da suke fuskanta.” In ji shi.
Ya kara da cewa bayan sun kada kuri’a, ya kamata su tsaya a wuraren zaben domin bibiyar yadda ake kirga kuri’un.
“Bayan sun fito sun kada kuri’a, su kuma tsaya, su raka tare da tabbatar da cewa an kirga kuri’un,” in ji shi.
Atiku ya yi magana kan lafiyarsa
An kuma tambayi dan takarar ADC game da lafiyarsa da kuma ko yana da karfin jagorantar Najeriya.
Atiku ya dage cewa yana cikin koshin lafiya kuma yana da karfin da zai ba shi damar jagorantar kasar.
"Babu wani likita da ya bayyana cewa ban cancanta ba ta fuskar lafiya. Na san jikina, na san ina cikin koshin lafiya, kuma ba ni da wata matsala ko kadan.” In ji shi.

Source: Facebook
Atiku ya gorantawa Obasanjo
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake yin magana mai kaushi kan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Atiku ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba shi da karfin siyasa a Najeriya ko kadan.
Asali: Legit.ng
