Babban Dalilin da Ya Sa Amurka ba Za Ta Cire Najeriya daga Jerin Kasashen CPC ba

Babban Dalilin da Ya Sa Amurka ba Za Ta Cire Najeriya daga Jerin Kasashen CPC ba

  • Ɗan majalisar dokokin Amurka ya jaddada cewa bai kamata kasar ta cire Najeriya daga ƙasashen da ake zargi da take ’yancin addini ba
  • Riley Moore ya ce karuwar kashe Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna akwai buƙatar ci gaba da matsa wa Najeriya lamba
  • Ya yi wannan magana ne bayan farmakin da aka kai kwanan nan a jihar Filato, wanda ya yi ajalin mutane fiye da 20

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya dage cewa bai kamata Amurka ta cire Najeriya daga jerin ƙasashen da take zargi da tauye yancin addini (CPC) ba.

Moore ya jaddada cewa ya kamata Najeriya ta ci gaba da zama a cikin kasashen CPC bisa zargin tsananta wa Kiristoci ba, yana mai cewa ana ci gaba da samun hare-hare a yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan sayar da litar fetur a N200

Riley moore.
Dan Majalisar wakilan Amurka, Riley Moore Hoto: @RepRileyMoore
Source: UGC

Moore ya bukaci kare kiristocin Najeriya

Riley Moore ya bayyana haka ne a sakon da ya a shafinsa na X yayin da yake mayar da martani ga wata sanarwa daga Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka.

Ya goyi bayan kiran Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ga Gwamnatin Najeriya da ta kare al’ummomin Kirista bayan harin da aka kai a Plateau, yana mai cewa Abuja ta yi alkawarin yin hakan.

“Ba za mu iya cire sunan Najeriya daga jerin CPC ba yayin da ’yan ta’addan masu tsattsauran ra’ayin Musulunci ke ci gaba da wannan mummunan aika-sika kan Kiristoci.
“Gwamnatin Najeriya dole ta cika alkawurran da ta ɗauka na kare al’ummomin Kirista marasa laifi,” in ji ɗan majalisar.

Kasar Amurka ta yi Allah wadai

Moore na mayar da martani ne ga wata sanarwa daga ma'aikatar Amurka mai kula da harkokin Afrika, wadda ta yi Allah wadai da sabon harin da aka kai a jihar Plateau, inda aka kashe sama da mutane 24, yayin da wasu da dama suka ɓace.

Kara karanta wannan

'Jahilci ke damunsu': Matashi ya kare kalaman Jingir kan Tinubu, Muslim Muslim

“Amurka ta firgita matuƙa da sake samun wani mummunan hari a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya, inda aka kashe mutane da dama da ke barci a gidajensu a jihar Plateau.
“Wannan lamari ya fi tayar da hankali saboda ya zo ne bayan taron CPC Working Group na baya-bayan nan.
"Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda aka kashe da waɗanda suka ɓace, tare da yin kira ga Gwamnatin Najeriya da ta cika alkawurranta na kare al’ummomin Kirista da kuma hukunta waɗanda ke aikata tashe-tashen hankula,” in ji sanarwar.
Trump da Tinubu.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sababbin kalaman Moore da hukumar Amurka sun nuna cewa wasu ’yan majalisar dokokin Amurka na ƙara matsa wa gwamnatin Shugaba Donald Trump lamba ta sake duba matsayin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta sha musanta cewa ana kai hare-haren ne saboda addini, tana bayyana rikice-rikicen a matsayin waɗanda suka fi karkata kan batutuwan ƙasa, albarkatun ƙasa da aikata laifuka.

Najeriya da Amurka sun sake zama

A wani labarin, kun ji cewa tawagar kasashen Najeriya da Amurka sun fara sabon zagaye na tattaunawa kan batun tsaro da yaki da ta’addanci a birnin Washington DC.

Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa kasar Amurka domin halartar taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262