Barazanar Trump Ta Ki Tsorata Iran, Jamhuriyar Musulunci Ta Yi Martani Mai Zafi
- Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi watsi da shirin Donald Trump na kakaba wa Tehran takunkumin tattalin arziki, yana mai cewa ci gaba ne da “manufofin da suka gaza”
- Araghchi ya ce manufofin Amurka za su jawo wa Washington karin shan kaye da kiyayyar al’ummar Iran
- Trump ya ce Amurka za ta kaddamar da wani mataki na tattalin arziki da ware Iran wanda ya kira mafi tsanani da aka taba dauka kan kowace kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, a ranar Alhamis ya yi watsi da shirin Shugaban Amurka Donald Trump na kakaba wa Tehran wani sabon takunkumi kan tattalin arziki.
Abbas Araghchi ya bayyana cewa hakan ci gaba ne da “manufofin da suka gaza” da za su jawo wa Washington karin shan kaye.

Source: Getty Images
Araghchi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Alhamis, 20 ga watan Agustan 2026.
Ministan ya ce abin da Trump ya kira “Economic D-Day” wani yunkuri ne na karkatar da hankali daga matsalolin tattalin arzikin Amurka da kanta, musamman bashin da ya kai wani mataki da ba a taba gani ba da kuma karuwar kudin ruwa.
Ya ce kara dogaro da manufofin da suka gaza zai jawo wa Amurka karin shan kaye da kuma kiyayyar al’ummar Iran.
Araghchi ya kara da cewa, “ta’addancin tattalin arzikin Amurka na barazana ga tattalin arzikin duniya da kuma ikon kasashe na tafiyar da harkokinsu.”
Donald Trump ya bayyana sabon shiri
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce yana sanar da “aikin tattalin arziki mafi murkushewa da aka taba dauka kan kowace kasa”.
Ya ce matakin zai kasance wani nau’in yakin tattalin arziki da ware Iran “a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba”.
Trump ya gargadi duk wata kasa da ta bari cibiyoyin hada-hadar kudi, kamfanoni, filayen jiragen sama ko hukumomin gwamnati su samar wa Iran da kowace irin hanyar ci gaba da gudanar da ayyukanta, yana mai cewa ita ma za ta fuskanci “babban hukuncin tattalin arziki”.
Yadda rikicin Iran da Amurka ya fara
Yaki ya barke tsakanin Iran da Amurka a ranar 28 ga Fabrairu bayan hare-haren Amurka da Isra’ila, lamarin da ya sa Iran ta mayar da martani a sassa daban-daban na yankin.
Tsagaita wutar da aka cimma a ranar 8 ga Afrilu ya kawo karshen mummunan ruwan bama-bamai, sai dai an ci gaba da samun arangama lokaci-lokaci a ciki da kewayen mashigar Hormuz.
Mashigar Hormuz wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi ce, kuma Iran ta rufe ta, lamarin da ya mayar da yankin daya daga cikin wuraren da rikicin ya fi yin zafi.

Source: Twitter
Iran ta gargadi makwabtanta
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Iran ta gargadi kasashen da ke gabar Tekun Fasha kan taimakawa sojojin Amurka.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa duk wani taimako da aka ba su zai zama tamkar shiga cikin ayyukan sojin Amurka.
Asali: Legit.ng

