Manyan Labarai A Yau
NiMet ta yi hasashen yanayi daban-daban na tsawon kwanaki uku, ciki har da hasken rana, gajimare, tsawa da ruwan sama a sassan kasar daga Litinin zuwa Laraba.
Kamfanin hada hadar kudi ta yanar gizo, Opay, ya bayyana cewa rahoton da ake yadawa a midiya cewa zai daina aiki a watan Satumba, 2026 ba gaskiya ba ne.
Labaran kanzon kurege sun cika shafukan sada zumunta a makon da ya gabata. Rahoton nan ya tattaro karyayyakin da muka ci karo da su a a Facebook, WhatsApp, da X.
Dakarun rundunar Operation Fansan Yamma ta kashe wani fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda mai suna Smally a Katsina tare da kwato makamai da alburusai.
Wasu 'yan mata guda uku daga gida ɗaya sun rasu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a Tiga Dam da ke jihar Kano. Shugabar karamar hukuma ta yi ta'aziyya.
Hukumar TETFund ta bukaci malaman manyan makarantun gaba fa sakandire da du cike bayanansu a shafin sabon zagayen tallafin NRS, ta fadi ranar da za a rufe.
Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC na Rantan, Garba Buba, da wani mazauni, yayin da hare-haren garkuwa da mutane ke ƙara tsananta a jihar Kano.
Kwamishinan Matasa da Wasanni na Borno, Sainna Buba, ya janyo cece-kuce bayan yin barazanar cutar da masu adawa da APC da kuma hana su amfana ta gwamnati.
Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya dakatar da ayyukan wata ƙungiya mai ikirarin Hisbah a Jos North, yana mai cewa ayyukanta ba su da izinin doka
Manyan Labarai A Yau
Samu kari