An Daina Amfani da Tsohuwar Takardar N100 a Najeriya? CBN Ya Yi Bayani

An Daina Amfani da Tsohuwar Takardar N100 a Najeriya? CBN Ya Yi Bayani

  • Bankin CBN na Najeriya ya tabbatar da cewa tsohuwar takardar N100 tana nan a matsayin halastaccen kuɗi
  • Babban bankin ya ce har da takardar N100 ta cika shekaru 100 na hadewar Najeriya dukkansu ana kashe su
  • Bankin CBN ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya ƙi karɓar takardar N100 zai fuskanci hukunci daidai da tanadin da doka ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa tsohuwar takardar kuɗin N100 ta yau da kullum tana nan a matsayin halastaccen kudi.

Babban bankin ya bayyana cewa dole ne a karɓe ta wajen gudanar da duk wata mu'amalar kudi a faɗin ƙasar nan.

CBN ya ce ana amfani da tsohuwar N100
Olayemi Cardoso da tsohuwar takardar N100 Hoto: @cenbank, @Sulaima43450532
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan sadarwa na CBN, Hakama Sidi-Ali, ta fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya hukunci a shari'ar da hukumar EFCC ta nemi ƙwace kadarorin Malami

Babban bankin ya ce ya lura da rahotannin da ke cewa wasu mutane da 'yan kasuwa sun fara ƙin karɓar takardar N100 saboda shakku kan ingancinta.

CBN ya fayyace matsayin takardun N100

CBN ya bayyana cewa takardar N100 ta yau da kullum da kuma takardar N100 ta tunawa da cika shekaru 100 da haɗewar Najeriya, dukkansu halastattun kuɗi ne da doka ta amince da amfani da su.

"Domin kawar da duk wani ruɗani, CBN na sake jaddada cewa takardar N100 ta tunawa da cika shekaru 100 na Najeriya, da kuma takardar N100 ta yau da kullum, dukkansu halastattun kuɗi ne a Najeriya kuma dole ne a karɓe su wajen duk wata mu'amala a faɗin ƙasar."
"Takardar N100 ta tunawa da cika shekaru 100 da Najeriya ba ta maye gurbin takardar N100 ta yau da kullum ba."

- Hakama Sidi Makama

CBN ya yi gargaɗi ga masu ƙin karɓar N100

Babban bankin ya yi gargaɗi ga daidaikun mutane, 'yan kasuwa, cibiyoyin kuɗi da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziƙi da su daina ƙin karɓar takardar N100 ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

CBN ya bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa tanade-tanaden dokar CBN, kuma duk wanda aka kama da wannan laifi zai fuskanci hukuncin da ya dace.

"CBN na ci gaba da jajircewa wajen kare martabar Naira, tabbatar da amincewar jama'a da duk takardun kuɗin da ya fitar bisa ƙa'ida, da kuma inganta zagayawar kuɗi cikin sauƙi a faɗin ƙasar."

- Hakama Sidi Makama

CBN ya ba jama'a shawara

CBN ta buƙaci al'umma su ci gaba da karɓa da amfani da dukkan takardun kuɗin da bankin ya fitar bisa doka.

Haka kuma ta shawarci duk mai buƙatar ƙarin bayani kan wannan batu da ya tuntubi bankin ta hanyoyin sadarwarsa na hukuma.

CBN ya warware zare da abawa kan takardun N100
Shugaban babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso Hoto: @cenbank
Source: Twitter

Tarihin sabuwar takardar N100

Jaridar TheCable ta ce a shekarar 2014, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ƙaddamar da takardar N100 ta musamman.

Shugaba Jonathan ya kaddamar da ita ne domin tunawa da cika shekaru 100 da haɗewar Najeriya zuwa ƙasa guda.

CBN ya soke lasisin wasu bankuna

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ba zai lamunci bankuna su jefa kudin da jama'a ke ajiyewa cikin garari ba.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Atiku ya tsoma baki, ya ba Tinubu wa'adi don gano gaskiya

Bisa hakan ne babban bankin ya sanar da soke lasisin wasu bankuna biyu na bangaren ba da rance da ajiyar kudi don mallakar gida a Najeriya.

CBN ya ce bankunan da lamarin ya shafa sun gaza a bangarori da dama, ciki har da mafi karancin jarin aiki da doka ta kayyade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng