Manyan Kwamandojin Boko Haram Sun Mika Wuya, Sojoji Sun Tatsi Muhimman Bayanai

Manyan Kwamandojin Boko Haram Sun Mika Wuya, Sojoji Sun Tatsi Muhimman Bayanai

  • Wasu manyan kwamandojin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai
  • Kwamandojin wadanda aka bayyana cewa sun rike muhimman mukamai a kungiyar, sun isa birnin Maiduguri inda aka tsare su
  • Dakarun sojoji sun samu muhimman bayanan sirri kan yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta bayan an yi masu tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Wasu karin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram guda biyu, wadanda manyan shugabanni ne da aka gano a matsayin ‘Munzirs’ sun mika wuya ga dakarun sojoji.

Kwamandojin na Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sashe na 2 na hadakar rundunar tsaro ta Arewa Maso Gabas, wato ‘Operation Hadin Kai’ (OPHK) a yankin karamar hukumar Geidam da ke jihar Yobe.

Kwamandojin Boko Haram sun mika wuya
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin kakakin rundunar OPHK, Kyaftin Mohammed Goni a fitar a ranar Talata, 7 ga watan Yulin 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kori mutanen kauyuka 30 a Sokoto, manya sun dauki mataki

Kwamandojin Boko Haram sun mika wuya

Tuni dai ‘yan ta’addan da suka mika wuyan suka isa birnin Maiduguri, kuma a halin yanzu suna hannun jami'an tsaro inda ake tantance bayanansu daki-daki, ana yi musu tambayoyi tare da amfani da bayanan sirri da aka samu daga gare su.

"Rundunar Operation Hadin Kai ta sake samun wata gagarumar nasara a yakin da ake yi da ta'addanci, biyo bayan mika wuya da manyan kwamandoji biyu suka yi ga dakarun sashe na 2 a Geidam a ranar 4 ga Yuli, 2026."

"Yan ta’addan da suka mika wuyan, wadanda aka gano su a matsayin ‘Munzirs’ a cikin tsarin shugabancin ‘yan ta’addan, sun isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kuma a halin yanzu suna hannun sojoji inda ake gudanar da cikakken bincike kan bayanansu, yi musu tambayoyi da kuma amfani da bayanan sirri.”

- Kyaftin Mohammed Goni

An samu muhimman bayanai a hannunsu

A cewar Goni, binciken farko ya nuna cewa kwamandojin biyu da suka mika wuyan sun rike manyan mukamai na fada a ji, kuma suna da dumbin sani game da ayyukan kungiyar, tsarin ba da umarni, da kuma dabarun tafiyar da kayan aiki."

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: An yi jana'izar basaraken 'yan bindiga suka kashe a jihar Sakkwato

“Bayanan sirri na farko da aka samu daga tambayoyin sun ba da haske mai muhimmanci game da hanyoyin gudanar da ayyukan ‘yan ta’addan, dabarun dorewar ayyukansu, da kuma hanyoyin samun tallafi."
“Ana sa ran wannan bayani zai taimaka kwarai da gaske wajen inganta ayyukan tsaro na yanzu da suka dogara da bayanan sirri, wadanda aka tsara domin gano wurare, dagula lissafi, da kuma tarwatsa sauran sansanonin ‘yan ta’adda da suka rage a fadin yankin Arewa Maso Gabas.”

- Kyaftin Mohammed Goni

Kwamandojin Boko Haram sun mika wuya
Manyan kwamandojin Boko Haram 2 da suka mika wuya Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An horas da sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an horar da sojojin Najeriya domin gudanar da aikin samar da tsaro da yaki da miyagu.

Babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa rundunar da yake jagoranta ta riga ta horas da sojoji 14,000.

Ya bayyana cewa suna daga cikin sababbin sojoji 28,000 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a dauka a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng