'Dalilin da Ya Sa Majalisar Dattawa Ta Amince da Kasafin N1.3bn don Ma'aikatar Bogi'

'Dalilin da Ya Sa Majalisar Dattawa Ta Amince da Kasafin N1.3bn don Ma'aikatar Bogi'

  • Majalisar Dattawa ta bayyana cewa ba ta saka Naira biliyan 1.3 ga hukumar PFIPC da gwamnati ta ce ba ta san da ita ba a kasafin kudin 2026
  • Kakakin majalisar Yemi Adaramodu ya ce ba aikin majalisar ba ne ta gudanar da binciken tsaro kan wadanda aka nada mukamai a ma'aikatun gwamnati
  • Adaramodu ya kara da cewa rigimar ta shafi ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da wanda ake zargi watau Adeniyi Adeyemi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawar Najeriya ta yi bayani kan sanya Naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kudin shekarar 2026 na ma'aikatar bogi ta PFIPC.

Majalisar Dattawan ta bayyana cewa ba ta da hannu wajen sanya Naira biliyan 1.3 ga hukumar da ake kira PFIPC, a cikin kasafin kudin shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Duk da zargin badakala, Tinubu ya naɗa Gbajabiamila cikin kwamitin ƴan sandan jihohi

Majalisar dattawa ta yi magana kan ma'aikatar bogi
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Kakakin majalisar, Sanata Yemi Adaramodu, ya yi wannan bayanin a ofishinsa da ke ginin majalisar a ranar Talata, 7 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Me majalisa ta ce kan ma'aikatar bogi?

Ya kara da cewa doka ta kundin tsarin mulkin kasa ba ta hau kan majalisar ta gudanar da binciken tsaro kan duk wanda ake nada shi ya jagoranci wata hukuma ko ma'aikatar gwamnati, saboda haka ba za a dorawa majalisar laifi kan wannan lamari ba.

“Shi wannan sashe na kasafin kudin da ake magana a kai, Majalisar Dokoki ta Kasa ba ita ta samar da shi ba ko shigar da shi ba, kuma ba aikin Majalisar Dattawa ko na Majalisar Wakilai ba ne su gudanar da binciken tsaro a kan wadanda aka nada su domin jagorantar hukumomin gwamnati."

- Sanata Yemi Adaramodu

Majalisar Dattawa ta tsame hannunta

Sanata Adaramodu, wanda ke wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu, ya bayyana cewa rigimar ta shafi bangaren zartarwa ne musamman tsakanin ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da wanda ake zargin ya yi amfani da takardu na jabu, Adeniyi Adeyemi.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Adeniyi Adeyemi dai ya kasance yana gabatar da kansa a matsayin shugaban hukumar wadda gwamnati ta ce ba ta san da zamanta ba.

Sanata Yemi Adaramodu ya ce idan an aika wa majalisar kararraki daga kowane bangare, za a duba batun daga fuskar doka, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Majalisar Dattawa ta tsame kanta a badakalar ma'aikatar bogi
Kakakin Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Yemi Adaramodu Hoto: Sen. Yemi Adaramodu
Source: Twitter

Haka kuma kakakin majalisar ya tabbatar da cewa majalisar ba za ta tsoma baki a yanzu ba domin an riga an kai batun gaban kotu, kuma bai dace ta shiga cikin lamarin da yake hannun alkali ba.

Ya nuna cewa da dai majalisar ta tantance kuma ta amince da wanda ake zargin shugaban hukumar ne, to da akwai dalilin alakanta majalisar da rigimar. Sai dai tun da babu irin wannan tabbaci, to ba ta da wata alaka da lamarin.

Tinubu ya umarci a binciki ma'aikatar bogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gudanar da bincike kan ma'ikatar bogi ta PFIPC.

Mai girma Bola Tinubu ya ba da umarni ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan hukumar PFIPC.

Shugaba Tinubu ya umarci cewa a kammala binciken sannan a mika masa cikakken rahoto a kai a cikin tsawon kwanaki 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng