Kaduna Ta Ɗauki Zafi, Mutanen Gari Sun Sake Kama Mutum 2 Sun Masu Kisan Gilla
- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama mutum shida kan zargin hannu a kisan gillan da aka yiwa matafiya biyu a Birnin Yero
- Rahotanni sun nuna cewa mutanen gari sun zargi matafiyan da sata, lamarin da ya sa suka kama su suka kashe
- Kwamishinan 'yan sandan Kaduna ya yi Allah wadai da lamarin tare da alƙawarin gurfanar da duk masu hannu a kisan a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Rundunar 'yan sandan Kaduna ta tabbatar da cafke mutane shida da ake zargi da hannu a kisan wasu mutum biyu da ke tafiya a kan babur a ƙauyen Gidan Kalu da ke Birnin Yero, kusa da Maraban Jos.
Mutanen da aka kashe sun hada da Muhammadu Sani mai shekaru 45 da Aliyu Mohammed mai shekaru 40, dukkaninsu mazauna ƙauyen Umar da ke karamar hukumar Igabi.

Source: Twitter
Rahotannin da Vanguard ta ruwaito sun ce suna kan hanyarsu ta zuwa Tudun Wada a Zariya domin duba wani ɗan uwansu da ke jinya lokacin da lamarin ya faru a ranar 1 ga Yulin 2026.
Yadda aka kashe mutum 2 a Kaduna
A cewar rundunar 'yan sanda, mutane sun fara zarginsu ne bayan sun gansu s kan sabon babur, inda suka yi ihu suna zarginsu da sata.man
Rahotanni sun nuna cewa matafiyan sun yi ƙoƙarin tserewa bayan sun bar babur ɗin, amma jama'a suka bi su, suka kama su tare da dukan su har lahira duk da roƙon da suka yi cewa ba su da laifi.
Wannan na zuwa ne makonni kadan kisan gillan da aka yi wa wata malamar Islamiyya, Ummulkhairi Usman Aliyu a Maraban Jos, jihar Kaduna.
'Yan sanda sun kama mutum shida
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce jami'an ofishin Birnin Yero sun isa wurin da lamarin ya faru tare da cafke Abdullahi Mukailu Kigo da wasu mutum biyar.
Ya ce wadanda ake zargin suna hannun 'yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike tare da kokarin cafke sauran mutanen da suka shiga cikin harin.

Source: Original
Kwamishinan 'yan sanda ya yi Allah wadai
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Muhammad, ya yi kakkausar suka kan kisan, yana mai bayyana shi a matsayin dabbanci da kuma karya doka.
Ya tabbatar da cewa za a kamo tare da gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a lamarin bisa tanadin doka.
Har ila yau, ya gargadi al'umma da su daina daukar doka a hannunsu, yana mai jaddada cewa hakan babban laifi ne, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Kiristoci sun yi tir da kisan Ummulkhairi
An ji cewa shugabannin kiristocin Arewacin Najeriya sun kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu, matar aka kashe a Marabar Jos ta jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar kiristocin Arewa ( NCA ), Fasto Joseph John Hayab, ya ce dole ne 'yan Najeriya su yi watsi da al'adar ɗaukar doka a hannu, yana mai jaddada cewa duk wanda ake zargi da wani laifi yana da haƙƙin samun adalci a gaban kotu.
Hayab ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro su tabbatar da kamo tare da gurfanar da duk waɗanda suke da hannu a kisan Malama Ummulkhairi.
Asali: Legit.ng

