'Yan Bindiga Sun Sake Hari a Sokoto, an Kashe Mutane da Jikkata Wasu

'Yan Bindiga Sun Sake Hari a Sokoto, an Kashe Mutane da Jikkata Wasu

  • Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Lajinge da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto
  • Mazauna yankin sun ce mutum shida sun mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a harin da aka kai da tsakar dare
  • Maharan sun kuma kwashe dabbobi masu yawa kafin su tsere, yayin da aka binne mamatan bisa koyarwar addinin Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto – Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe mutum shida tare da jikkata wasu biyar a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun yi ta'asar ne a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Lajinge da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce maharan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, inda suka ci gaba da kai farmaki har zuwa kusan ƙarfe 2:20 na dare.

Kara karanta wannan

Bayan malamar Islamiyya, An kona gawar mutumin da kashe a Kano

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun riƙa harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa al'ummar ƙauyen cikin firgici.

Maharan sun sace dabbobi

Baya ga kashe mutane da jikkata wasu, maharan sun kuma yi awon gaba da adadin dabbobin da ba a tantance ba kafin su tsere daga yankin.

Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana harin a matsayin abin takaici.

Ya bayyana cewa:

"Sun zo da yawa a kan babura sannan suka fara harbi ba tare da kakkautawa ba. Sun kashe mutum shida ciki har da wata matar aure, sannan suka jikkata wasu biyar."
"Ba su yi garkuwa da kowa ba a wannan harin. Dabbobinmu kawai suka kwashe. Waɗanda suka jikkata suna karɓar magani a asibiti."

An binne mamatan da aka kashe

An riga an binne mutanen da suka rasa rayukansu a harin na 'yan bindiga bisa koyarwar addinin Musulunci.

An bayyana sunayen waɗanda aka kashe kamar haka, Alhaji Dankane S/Ruwa, Samaila Isah Udu, Adare Dansisi Makeri, Danlami Abdulrahaman, Maryam Dankane da Hamisu Adamu

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ta'asa a Kogi, sun hallaka mutane da dama yayin hari

Waɗanda suka jikkata sun haɗa da Lawali Danjaji, Sani Ibrahim, Garba Adare Garbobo, Iliya Muntari da Adamu Yarkyeya

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ba a samu tabbacin hukuma ba

Ƙoƙarin samun tabbaci daga hukumomi bai yi nasara ba, domin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a samu amsa daga 'yan majalisar da ke wakiltar yankin ba.

Hakazalika, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto bai dauki kiran wayar da aka yi masa ba.

'Yan bindiga sun yi barna a Kogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe aƙalla mutum bakwai a wani sabon hari da suka kai garin Okele-Ejule da ke ƙaramar hukumar Ofu a jihar Kogi.

'Yan bindigan sun sanya kayan sojoji, sannan suka kutsa cikin garin, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da zaɓe ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Wasu majiyoyi daga yankin sun yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda aka kashe suna da tarihin aikata laifuffuka, yayin da wasu kuma ke ganin akwai alaƙar siyasa da harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng