Magana Ta Fito: Adeniyi Ya Bayyana Dalilin Kafa Ma'aikatar Bogi Ta PFIPC

Magana Ta Fito: Adeniyi Ya Bayyana Dalilin Kafa Ma'aikatar Bogi Ta PFIPC

  • Adeniyi Adeyemi ya ce ya kafa hukumar PFIPC ne saboda kishin ƙasa da burin jawo masu zuba jari zuwa Najeriya
  • Ya musanta cewa yana da wata manufa ta kashin kansa, yana mai cewa burinsa shi ne ya tallata Najeriya da gwamnatin Bola Tinubu
  • Adeyemi ya ce bai san yadda aka saka kasafin kuɗin hukumar cikin kasafin kuɗin ƙasa ba saboda yana tsare a lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi Matthew, ya yi sababbin maganganu kan takaddamar da ake yi.

Adeniyi Adeyemi wanda ke cikin ce-ce-ku-ce, ya bayyana dalilin da ya sa ya kafa hukumar da yanzu ba ta ci gaba da aiki.

Adeyemi ya fadi dalilin kafa hukumar PFIPC
Shugaban hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Adeniyi Adeyemi Matthew ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta kiran bidiyo, Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), a ranar Talata, 7 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Yadda Adeniyi Adeyemi ya yi magana da Gbajabiamila

Ya ce babban abin da ya ƙarfafa shi shi ne kishinsa ga Najeriya, burin jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma tallata gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ba don wata riba ta kashin kansa ba.

Adeyemi ya ce kishin ƙasa ya sa ya kafa PFIPC

Adeyemi ya kuma yi ikirarin cewa bai san yadda aka saka kasafin kuɗin hukumar da kuma yadda aka kare shi a Majalisar Tarayya ba, duk da cewa shugaban ƙasa ya amince da kasafin.

"Na kafa wannan hukuma, tare da kashe kuɗin da ake ta magana a kai (kimanin naira miliyan 400), ne saboda kishin ƙasata. Burina shi ne na kawo masu zuba jari daga ƙasashen waje zuwa Najeriya domin na bar tarihi mai kyau. Abin da kawai nake so shi ne na yi wa ƙasata hidima."
"Saboda haka na kashe kuɗin. Ina son in taka rawa ta wajen ci gaban ƙasa. An kafa wannan hukuma ne domin jawo masu zuba jari zuwa Najeriya da kuma sanya ƙasar ta zama ɗaya daga cikin wuraren da masu zuba jari suka fi so."

- Adeniyi Adeyemi

Dalilinsa na yi hulda da ma'aikatun gwamnati

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Shugaban hukumar da ake zargi zai taimakawa binciken ICPC

Adeyemi ya ce ya yi hulɗa da ma'aikatun gwamnati daban-daban, hukumomi da kuma hukumar EFCC domin inganta martabar Najeriya a idon masu zuba jari, jaridar TheCable ta kawo labarin.

"Ba batun wata riba ta karan kaina ba ne. Kafin wannan takaddama ta ɓarke, muna shirin gudanar da wani babban taron ƙasa da ƙasa domin jawo hankalin duniya zuwa Najeriya."

- Adeniyi Adeyemi

Adeniyi Adeyemi ya yi magana kan kafa hukumar PFIPC
Adeniyi Matthew Adeyemi da ke ikirarin shugabantar hukumar PFIPC Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Ya yi tambaya kan kasafin kuɗin hukumar

Da yake mayar da martani kan matsayar fadar shugaban ƙasa cewa ba ta san da hukumar ba, Adeyemi ya ce hakan ya ba shi mamaki.

"Wannan lamari yana da ruɗani, musamman idan fadar shugaban ƙasa ta ce babu wannan hukuma. Ta yaya kuma kasafin kuɗinta ya shiga cikin kasafin kuɗin ƙasa?"
"A gaskiya ma ina tsare na tsawon kwanaki 23 lokacin da aka shirya tare da kare kasafin kuɗin PFIPC a Majalisar Tarayya tsakanin Oktoba da Nuwamba."

- Adeniyi Adeyemi

Adeyemi ya yi magana da Gbajabiamila

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa ya yi magana da Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Gwamnatin tarayya ta rage harajin shigo da motoci zuwa Najeriya

Adeniyi ya bayyana cewa ya yi magane da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ne ta hannun marigayi abokinsa, Dolapo Tanimola.

Ya ce bai taɓa haɗuwa da Gbajabiamila ido da ido ba, ko kafin ko bayan abin da ya kira naɗa shi a matsayin shugaban hukumar PFIPC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng