2027: Pantami Ya Fadi Abubuwan da zai Yi wa Gombe idan Ya Zama Gwamna

2027: Pantami Ya Fadi Abubuwan da zai Yi wa Gombe idan Ya Zama Gwamna

  • Yayin da ya ke magana game da siyasar 2027 da ake fuskanta a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya ce gwamnatocin baya sun yi wasu muhimman ayyuka a jihar Gombe
  • Dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Pantami ya ce abin da jihar ke bukata a yanzu shi ne mayar da hankali kan inganta rayuwar al’umma
  • Pantami ya ce ya kamata a fi mayar da hankali kan gina ɗan Adam ta hanyar ingantaccen ilimi, kyautata rayuwar malaman makaranta da ƙarfafa mata da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar GombeSheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci ga jihar Gombe a wannan lokaci shi ne mayar da hankali kan inganta rayuwar al’umma da gina ɗan Adam.

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba

Pantami ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wa wasu ɗalibai da suka kai masa ziyara, inda ya ce gwamnatocin baya sun yi abubuwa masu muhimmanci wajen ci gaban jihar.

Sheikh Isa Ali Pantami
Dan takarar PDP a Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

A wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, Pantami ya ce ba a samu kulawa sosai ba wajen gina mutane saboda an fi mayar da hankali kan gina birane da abubuwan more rayuwa fiye da bunƙasa ɗan Adam.

Pantami ya fifita gina ɗan Adam

Pantami ya ce duk da muhimmancin gine-gine da samar da abubuwan more rayuwa, ya kamata a fahimci cewa ɗan Adam shi ne mafi daraja cikin halittun Allah.

Ya ce Abin da zan fi ba wa muhimmanci shi ne inganta rayuwar al’umma. Ind ya ce an bar jihar a baya wajen gina mutane, domin an fi mayar da hankali kan gina birane fiye da gina ɗan Adam.

A cewarsa, ya kamata tsarin ci gaban jihar ya mayar da hankali kan samar da mutanen da za su iya amfani da ilimi da ƙwarewarsu wajen kawo sauyi a cikin al’umma.

Maganar inganta ilimi

Farfesan ya ce inganta rayuwar al’umma yana farawa ne daga ilimi, inda ya jaddada muhimmancin samar da ingantaccen ilimi daga matakin firamare zuwa sakandare da jami’a.

Kara karanta wannan

"Na ji kunya": Tinubu ya ba EFCC umarnin bude asusun gwamnatin Osun da aka rufe

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a wajen taron PDP. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Sheikh Isa Ali Pantami ya ce ba za a samu ingantaccen ilimi ba matuƙar ba a horar da malamai yadda ya kamata ba.

A cewarsa, ya kamata a ba malamai horo, tarbiyya da ƙwarewar da za su ba su damar koyar da ɗalibai cikin kwarewa da natsuwa.

Pantami ya kuma jaddada muhimmancin kula da haƙƙin malamai, musamman ta fuskar albashi da alawus-alawus.

Pantami zai ƙarfafa mata

Pantami ya bayyana rashin bai wa iyaye mata damar taka rawar da ta dace a wasu muhimman al’amuran al’umma a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce a ganinsa, bai wa mata dama da ƙarfafa su na iya zama mafi muhimmanci fiye da gina jami’o’i kawai, saboda mata suna taka muhimmiyar rawa wajen gina iyali da tarbiyyar yara.

PDP ta kare Pantami kan rikicin Rarara

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta yi Allah-wadai da kalaman da ta bayyana a matsayin na cin mutunci da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya yi kan Pantami.

Kara karanta wannan

Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Jam’iyyar ta ce kalaman da ke cikin wata sabuwar waƙar Rarara sun kasance na ɓata suna da rashin mutunci, tana mai cewa bambancin siyasa bai kamata ya zama dalilin cin mutuncin mutane ba.

PDP ta kuma bayyana Pantami a matsayin malamin addinin Musulunci kuma Farfesa da ya sanu a duniya, tana mai cewa ya cancanci a mutunta shi ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng